Monday, March 2, 2020

TAKAITACCEN TARIHIN YA'YAN ANNABI (S.A.Ws) MAZA

TAKAITACCEN TARIHIN YA'YAN ANNABI (S.A.Ws) MAZA

Annabi (S.A.Ws) yana da 'ya'ya maza uku, mata hudu. Dukkan ' ya'yansa ya same su ne wajen Khadijah (R.Ah) in banda dansa Ibrahim. Qasim shi ne baban dansa na farko, da aka haifa masa kafin fara saukar wahayi. Ya rasu a lokacin yana shekara biyu.

Dansa na biyu Abdullah, an haife shi bayan fara saukar wahayi. Don haka daga baya ake kiransa Tayyab da kuma Tahir. Shima ya rasu yana dan yaro. Alokacin rasuwarsa Kuraishawa sun yi ta murna suna cewa:
Muhammadu ba shi da (namiji), don haka ba shi da wanda zai gaje shi. Don haka sunansa zai 6ace bayan mutuwarsa.

A saboda haka ne Allah (Subhanahu wa Ta'ala) ya saukar da suratul Kauthar 1-3)

Dansa na uku, kuma na karshe, Ibrahim, an haife shi ne a Madinah, a shekara ta 8 bayan Hijirah. Baiwar Annabi (S.A.Ws) Mariya ita ce ta haifa masa yaron. An yanka raguna guda biyu, sa'annan wani Sahabi da ake kira Abu-Hind Bayazi (R.A) shi ne ya aske kan yaron, kana daga baya aka bayar da azurfa daidai nauyin sumarsa a matsayin sadaka, sa'annan aka binne sumar.

Annabi (S.A.Ws) ya ce:
Zan baiwa da na sunan kakana, Ibrahim (As).
Shima wannan yaron ya rasu ranar 10 ga watan Rabi'ul-Awwal, shekara ta goma, bayan Hijirah. Alokacin yana da watanni 18 kadai a duniya. Manzon Allah (S.A.Ws) ya ce:

Allah Ta'ala Ya nada wata mai reno, da za ta lura da Ibrahim a cikin lambunan Aljannah.

Insha Allahu rubutu na gaba akan 'Ya'yan Annabi (S.A.Ws), Mata amma kafinnan zan danyi tsokaci akan mai kirma Gwamnan Borno. Muna kuma rokon Allah ya gafarta mana kurakuranmu ya kuma sa Aljannar Firdausi itace makomarMu baki daya. Aameen ya Qadiyal Haajah.

No comments:

Post a Comment