SHIN KO KA KASAN CE ACIKINSU?
An rawaito daga Hadisin farju bn Farralata, daga Abu Jablatu, daga Saidu bn Musayyib, daga Abudur Rahman dan Samrata (RA) Yace; Wata Rana manzon Allah (saww) ya fito zuwa gare mu, mu kuma muna zaune. Sai yace mana, lallai ni jiya naga abin mamaki!
Yace naga wani mutum daga cikin alummata, wanda yake mala'ikan mutuwa yazo masa don ya karbi Ransa, sai ga kuma biyayyar da ya ke yiwa iyayansa, sai Allah (swt) ya hana wannan mala'ikan mutuwa daukar ransa.
Kuma naga wani mutun shaidanu (Aljannu) sun kewaye shi,kawai sai ga zikirinsa da yakeyi yazo sai shaidanun nan suka tsere daga wannan mutum.
Naga wani mutum daga cikin alummata, hakika mala'ikkun azaba sun kewayeshi, sai kawai ga Sallar sa, sai wadannan kayan azaba dake hannun wadannan mala'ikkun yazama babu su.
Naga wani mutum daga cikin alummata, yana ta zaro harshe saboda tsananin jin kishin da yake ji, amma duk sanda ya matso wajan shan ruwa sai a koreshi, a hanashi, sai ga Azumin sa yazo
ya shayar dashi, ya kosar dashi.
Naga wani mutum daga cikin alummata, kuma naga Annabawa, a zaune ga sunan wasu bayan wasu, amma daya kusanto sai a koreshi, ahanashi zuwa wajen, amma kawai sai ga wankan shi na janaba yazo, sai ya kama hannunsa ya zaunar dashi gefen wadannan Annabawa din.
Naga wani mutum daga cikin al'ummata, gabansa, da bayansa duhu, gefan hagu dana dama duhu, kai hatta saman sa ma duhu ne,gashi kuma ya dumaice acikin wannan duhu, kawai sai ga Hajjin sa da ummarar sa suka fitar dashi daga cikin wannan duhun, suka kuma shigar dashi cikin Haske.
Naga wani mutum daga cikin alummata, yana jin tsoron wuta, da kuma harshen ta, da sharrinta, sai ga gaskiyar sa tazo, sai ta zama garkuwa tsakaninsa da wannan
wutar, kuma tayi masa inuwa asaman kansa.
Naga wani mutum daga cikin alummata, yana yiwa muminai magana, amma su kuma basa yi masa maganar, sai ga sadar da
zumuncinsa yazo, yace ya sanar da musulmai lallai shiya kasance yana sadar da zumunci, kuyi masa magana mana, kawai sai suka yi masa magana suka gaisa dashi shima ya gaisa dasu.
Naga wani mutum daga cikin al'ummata wanda yake mala'ikkun wuta zabbaniyawa sun kewaye shi, sai ga umarni da kyawawa da ya keyi, da kuma hani ga mummuna da ya keyi sunzo kawai sai ya zama wannan kayan azabar na hannun su babusu, sai Allah ya shigar dashi cikin mala'ikkun rahama.
A Duba a cikin littafin ARRUH.
Shin ko ka kasance Kana Aikata wayannan abubuwan? Hakika idan baka Cikin masu aikatawa maza ka gyara domin ka samu kasancewa a cikinsu.
Ya Allah ka sa mu dage akan Yin Ayukka na Kwarai da Nagarta. Kuma ka kar6a mana ayyukan mu
Ka liking wannan link domin samun ingan tattun bayanai gameda addinin Musulunci.Ãmīn
.https://ahmadmusainc.blogspot.com/2020/02/shafin-wayr-da-kan-al-ummah.html?m=1
No comments:
Post a Comment