Thursday, February 20, 2020

BABU MAI IRIN BAIWAR ANNABI (S.A.Ws)


Sayyidina Umar (rta) yana cewa: Mun fita zuwa Yakin Tabuka tare da Manzon Allah (saww), a lokacin da ake cikin tsananin zafi mai kuna, mun ya da zango a wani wuri, kishi ruwa ya dame mu.

Mutum yakan fita don ya nemi ruwa, kafin ya dawo sai ya ji makogoransa kamar ya tsattsage, wasu sukan yanka rakumi su ciro tumbinsa su sha ruwan.

Sai Sayyidina Abubakar (rta) yace: Ya Manzon Allah (S.A.Ws)! Muna rokon ka da kayi mana addu’a.

Sai Ma’aikin Allah (S.A.Ws) ya daga hannayensa sama yana addu'a, ai kuwa kafin ya sauke hannayensa masu daraja, sararin samaniya ya
canja, hadari ya hado, ruwa ya tsinke, mutane suka sha suka cika abubuwan da ke tare da su.

Daga nan muka duba sai muka ga ruwan a iya inda muke kadai aka yi shi. (A duba aTafsirin Dabri: 14/541, Ibn Hibban: hadisi mai lamba1707, Hakim: juz'i na1/159 ya kuma inganta shi da shi da Ibn Kathir).

Yaa Allah ka karawa Annabi (S.A.Ws) daraja

No comments:

Post a Comment