Friday, December 8, 2023
TAMBAYA NA TARA (0009) SHIN MAI CIKI TANA YIN HAILA?
TAMBAYA NA TARA (0009) SHIN MAI CIKI TANA YIN HAILA?
Yawanci idan mace ta ɗau ciki jini yakan daina zuwa mata, Imamu Ahmad yana cewa (Mata suna gane samuwar ciki da yankewar jini) Idan mace mai ciki ta ga jini idan hakan ya kasance kafin haihuwa da kwana biyu ko uku kuma a tare da shi akwai ciwon haihuwa to wannan jinin haihuwa ne, idan kuma kafin haka ne da lokaci mai tsawo, ko kuma tsakaninsa da haihuwa ba yawa amma ba zafin haihuwa to wannan ba biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen haila ba za su shafe shi ba?
Anan Malamai sun yi saɓani: Abin da yake daidai shi ne jinin haila ne in dai ya zo a yadda ta saba yin jinin haila, saboda asali duk jinin da ya zowa mace ana ɗaukarsa a jinin haila, in dai ba akwai wani sababi da zai hana shi ya zama haila ba, kuma babu wani dalili a Alkur'ani ko a Sunna da zai hana shi ya zama haila. Wannan shi ne mazahabar Maliku da Shafi'i, kuma Baihaki ya hakaito hakan daga cikin maganganun Ahmad. Don karin bayani duba: Dima'uddabi'iyya shafi na 11.
Allah ne Mafi sani.
Don samun amsar tambaya na takwas ku shiga nan👉👇
YARJEJENIYAR HUDAIBIYA DA KUMA LABARIN ABU JANDAL DA KUMA ABU BASIR (R.A) KASHI NA ƊAYA
YARJEJENIYAR HUDAIBIYA DA KUMA LABARIN ABU JANDAL DA KUMA ABU BASIR (R.A) KASHI NA ƊAYA
Ashekarata shidda bayan Hijrahn Manzon Allah (S.A.Ws) tare da Sahabbansa, sun bar Madinah zuwa Makkah don yin Umrah, A lokacin da Ƙuraishawa suka samu labarin wannan zuwa nasu, sun yi ƙoƙarin hana shi shiga cikin Makkah duk da cewa aikin hajji yake shirin yi.
Don haka wannan abu ala tilas, tasa ya kafa sansani a Hudaibiyya. Sahabbansa su dubu daya da dari hudu (1400), sun (tsaya kai da fata cewar, lallai sai sun shiga Makkah, ko da za ta kaisu ga yin yaki ne. Amma ra'ayin Manzon Allah (S.A.Ws) a wannan lokaci ya sha bamban da nasu. Duk da cewar Sahabbansa shirye suke a gwabza yaki da su, maimakon haka ta faru, sai ma ya kulla yarjejeniya da Ƙuraishawa, kuma ya amince da dukkan sharuɗɗan da suka gicciya.
Wannan yarjejjeniya maras ma'ana a zahiri, wadda ta fi kyautatawa su Kuraishawa, ta yi matukar wahalar karba ga Sahabbai. Amma kuma cikakkar ɗa'arsu ga Manzon Allah (S.A.Ws) ta hana su hawa kujerar na ki a kan yarjejeniyar. Ko da jarumai irin su Sayyadina Umar (R.A) ala tilas, shima ya haƙura da irin shawarar da Annabi ya zartas.
Kamar yadda daya daga cikin ka'idodin wannan yarjejjeniya ya nuna; Mutanen da suka Musulunta a lokacin da ake kulla wannan yarjejeniyar, tilas ne a mayar da su hannun Kuraishawa. Amma su kuma Kuraishawan da suka gudu daga hannun Musulmi, ba za'a maida su ba.
Abu Jandal (R.A) wanda yake Musulmi ne a Makkah, Yana matukar shan wahala a hannun Kuraishawa. Kullun a ɗaure yake da sarkoki. Da ya sami labarin isowar Manzon Allah (S.A.Ws) Hudaibiyyah, ya samu ya kubuta, inda ya kurɗa har ya samu ya isa inda Musulmi suke, ana gab da rattaɓa hannu akan wannan yarjejjeniya. Mahaifinsa Suhail, (wanda a lokacin bai Musulunta ba), shi ne jakadan Kuraishawa a wajen wannan yarjejeniya, ya kaiwa Abu Jandal (R.A) mari, inda kuma ya tsaya kai da fata cewar, lallai sai ya koma da shi Makkah.
MU HAƊU A KASHI NA BIYU
Allah ya sa mudace alfarman fiyayyen halitta Annbi
✍️AHMAD MUSA
Ku shiga nan domin samun yadda Anas bin Nadr yayi shahada
👉👇
https://ahmadmusainc.blogspot.com/2023/12/shahadar-anas-bin-nadr-ra-kashi-na-biyu.html
Monday, December 4, 2023
SHAHADAR ANAS BIN NADR (R.A) KASHI NA BIYU
SHAHADAR ANAS BIN NADR (R.A) KASHI NA BIYU
A kashi na ɗaya mun tsaya a dai-dai inda
"Wannan umurni dai na Manzon Allah (S.A.Ws) kurum har zuwa lokacin da ake yin fada ne".
Don haka masu dawakai da suka hango babu wanda ke lura da baya, sai suka yunkuro a guje, inda suka samu suka kutsa, kana suka shammaci Musulmi ta baya, waɗanda suka dukufa wajen kwasar ganima. Ana cikin wannan hali ne fa, Anas (R.A) ya hango Sa'ad bin Ma'az (R.A) yana kokarin wucewa ta gabansa. Nan take ya yi masa tsawa, inda ya jawo hankalinsa yana mai cewa; 'Ya Sa'ad! Ina ka ke shirin zuwa? Na rantse da Allah Ta'ala, na jiyo kamshin Aljannah ya na kunnowa daga Dutsen Uhudu Ai kuwa faɗın haka keda wuya, sai ya yi kururuwa, inda ya yi tsalle, ya kutsa tsakiyar filin daga, aka yi ta ɗauki ba daɗi tare da shi, har sai da ya yi Shahadah. Bayan kammala yakin an yi daga-daga da jikinsa.
Inda aka yi ɗai-ɗai da shi. Wanda ta kai, sam babu wanda zai iya gane shi, sai kurum kanwarsa ce ta shaida shi, shima bayan da ta dubi yan yatsunsa. Irin rauninkan da aka yi masa wanda ya kama daga na kibbau zuwa na takubba, sun fi tamanin.
Don haka dai waɗanda suka yi jihadi fi sabilillah, tsakani da Allah, tare da juriya da hakuri, har kamshin Aljannah suke jiyowa tun daga nan duniya, kamar yadda wannan bawan Allah Anas (Radhiyallahu anhu) ya jiyo kamshin Aljannah
MU HAƊU A RUBUTU NA GABA AKAN
Yarjejeniyar Hudaibiyyah Da Kuma Labarin Abu Jandal Da Kuma Abu Basir (R.A).
Allah ya sa mudace alfarman fiyayyen halitta Annbin rahama Muhammad (S.A.Ws)
✍️ Ahmad Musa
Sunday, December 3, 2023
TAMBAYA NA TAKWAS (0008) A WANI SHEKARU NE MATA SUKE FARA YIN HAILA DAKUMA SHEKARUN DA SUKE DAINAWA
TAMBAYA NA TAKWAS (0008) A WANI SHEKARU NE MATA SUKE FARA YIN HAILA DAKUMA SHEKARUN DA SUKE DAINAWA
Yawancin mata suna fara yin haila ne daga shekara 12-50 amma wani lokacin mace tana iya yin haila kafin shekara 12 ko kuma bayan shekara 50, wannan ya danganci yanayinta da kuma wurin da take zaune, da abincin da take ci.
Malamai sun yi saɓani: shin akwai wata shekara ta musamman da mace take fara haila ko kuma take dainawa, ta yadda jinin da ya sameta kafin wannan ko bayan wannan shekarun ba za'a kira shi jinin haila ba?
Darimi -Allah Ya yi masa rahama-ya ce bayan ya ambaci saɓanin da aka yi: "Wannan duk kuskure ne a wajena, domin abin lura shi ne samuwar jinin, don baka duk lokacin da aka samu jinin a cikin kowacce shekara ne ya wajaba a sanya shi ya žarna haila", abin da Darimi ya faɗa shi ne daidai saboda Allah da ManzonSa sun rataya hukunce hukuncen jinin haila ne da samuwarsa, ba su kuma iyakance wasu shekaru na müsamman ba, kamar yadda aya ta (222) a suratul bakara take nuni zuwa hakan, wannan yake nuna mana iyakance shi da lokaci na musamman yana bukatar dalili ne daga litttafi Allah ko daga Sunnar ManzonSa, ba'a kuma samu ba.
Don neman karin bayani duba: Dima'uɗɗabi'iyya shafi na :6
Allah ne Mafi sani
Kushiga nan domin samun amsar tambaya na 0007
👉👇
https://ahmadmusainc.blogspot.com/2023/12/tambaya-na-0007-mecece-hukuncin.html
Saturday, December 2, 2023
TAMBAYA NA (0007) MECECE HUKUNCIN FUSKANTAR ALKIBLA YAYIN BIYAN BUKATA A BANDAKI ?
TAMBAYA NA (0007) MECECE HUKUNCIN FUSKANTAR ALKIBLA YAYIN BIYAN BUKATA A BANDAKI ?
To Malamai sun yi saɓani akan wannan hukuncin, Abu- hanifa ya hana hakan, Malik ya tafi akan cewa mutukar a gida ne to babu laifi, saboda hadisin Abdullahi dan Umar wanda yake cewa: "Na hau ɗakin Hafsa sai na ga Annabi (S.A.Ws) yana biyan bukatarsa, yana fuskantar Sham ya kuma juyawa alkibla baya", kamar yadda Bukari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (145).
Saidai abin da ya fi shi ne kar mutum ya fuskanci Alkibla, ko da a gida ne, saboda hadisin Abu-ayyub wanda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake cewa: "Idan kuka zo yin bahaya to kada ku fuskanci alkibla kada kuma ku bata baya" Bukhari a hadisi mai lamba ta: (394) d aMuslim a hadisi lamba ta: (264),
Tabbas barin kallon alkibla yayin biyan bukata shi ne ya fi, saboda hadisin da ya gabata da kuma fita daga sabanin Malamai, don haka idan mutum zai gina masai a gidansa zai yi kyau ya kautar da ita daga alkibla. Don neman karin bayani duba: Bidayatul-mujtahid 1\115. Allah ne Mafi sani
TAMBAYA NA SHIDA (0006) YAYA IDDAR MATAR DA BA TA YIN HAILA DUK WATA?
TAMBAYA NA SHIDA (0006) YAYA IDDAR MATAR DA BA TA YIN HAILA DUK WATA?
To yan'uwa dole ne, sai ta yi jini uku kamar yadda Hanafiyya suka fada, ko kuma tsarki uku kamar yadda Malikiyya suka tafi akai, ko da kuwa duk shekara take yin haila sau daya, saboda Allah Madaukaki ya rataya idda ne da samuwar jini, kamar yadda yake cewa a cikin suratul Bakara aya ta : (228)
"Kuma matan da aka saka, to za su jira tsawon jinane uku" Don haka duk tsawon lokacin da za ta zauna to dole sai ta jira su, kamar yadda ayar take nunawa.
Allah ne Mafi sani.
TAMBAYA NA BIYAR (0005) MECECE SIFFAR WANKAN JANABA?
TAMBAYA NA BIYAR (0005) MECECE SIFFAR WANKAN JANABA?
Yan'uwa janaba wani hukunci ne da yake faruwa saboda ɗaya daga cikin abubuwa guda biyu :
1. Ko dai mutum ya yi mafarki kuma ya ga maniyyi,
2. Ko kuma mutum ya sadu da matarsa, duka waɗannan suna wajabta wanka, wankan janaba tana da siffofi guda biyu, duk wacce ka ɗauka ta yi:
I/. Siffar da ta fi kamala ita ce wacce ta zo a hadisin A'isha cewa Manzon Allah (S.A.Ws) idan ya zo wankan janaba yana farawa ne da wanke hannunsa, sannan sai ya wanke farjinsa da hannun hagu, sai kuma ya yi alwala amma ban da wanke kafa, sannan sai ya ɗebi ruwa sau uku ya zuba a gashinsa, bayan haka sai ya zuba a ragowar jikinsa, sannan sai ya wanke kafarsa. Bukari da Muslim.
II/. Akwai kuma siffa ta biyu wacce ta zo a hadisin Ummu-salama lokacin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake siffanta mata wankan janaba, inda yake ce mata: "Ya isar miki ki zuba ruwa sau uku a kanki, sannan ki zuba a duka jikinki, mutukar kin yi haka to kin tsarkaka" Muslim ne ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (330). Allah ne Mafi sani.
Subscribe to:
Posts (Atom)