Saturday, December 2, 2023

TAMBAYA NA HUƊU (0004) MENE NE ABUBUWAN DA SUKE KAWO NUTSUWA A CIKIN ZUCIYA

TAMBAYA NA HUƊU (0004) MENE NE ABUBUWAN DA SUKE KAWO NUTSUWA A CIKIN ZUCIYA To yan'uwa akwai abubuwan da malamai suka yi bayani cewa, suna kawo nutsuwa a zuciya, ga su kamar haka: 1. Cikakken tauhidi, ta yadda mutum zai bar duk wata shirka da bidi'a da abin da yake kaiwa zuwa gare su.
2. Shiriya da hasken da Allah Yake jefawa a zuciyar bawa, wanda duk lokacin da aka rasa shi, sai bawa ya kasance cikin kunci. 3. Ilimi mai amfani, saboda duk lokacin da ilimin mutum ya yalwata, zai samu jindadi a zuciyarsa. 4. Dawwama akan zikirin Allah, saboda fadin Allah "Wadanda suka yi imani, zuciyoyinsu suna nutsuwa da zikirin Allah" Suratu Arra'ad aya ta (28). 5. Kyautatawa bayin Allah, saboda duk mutumin da yake yin kyauta zai kasance cikin kwanciyar hankali, kamar yadda marowaci yake kasancewa cikin kunci. 6. Fitar da kyashi da hassada daga zuciya. 7. Barin kallo da zancen da ba shi da fa'ida. 8. Barin baccin da ba shi da amfani. 9. Cin abinci gwargwadon bukata, da rashin karawa akan haka. 10. Rashin cakuduwa da mutane sai gwargwadon bukata. Kishiyoyin wadannan abubuwa su ne suke jawo bakin ciki da damuwa da kuma kunci. Don neman karin bayani duba zadul-ma'ad 2\22. Allah Ne Mafi sani.

Wednesday, November 29, 2023

TAMBAYA NA UKU (0003) MENENE BAMBANCI TSAKANIN MUNAFUNCIN ZUCIYA DA MUNAFUNCIN AIKI?

TAMBAYA NA UKU (0003) MENENE BAMBANCI TSAKANIN MUNAFUNCIN ZUCIYA DA MUNAFUNCIN AIKI? Malam, menene bambanci tsakanin nifakul amali da i'itikaadi? To Malam: Nifaqul i'itikadi (wanda ake kudurcewa a zuciya) shi ne boye kafurci da kuma bayyana Musulunci, kamar yadda wasu mutane suka yi a zamanin Manzon Allah (S.A.Ws), duk wanda ya siffantu da wannan to ba musulmi ba ne, kamar yadda Allah ya yi bayani a suratul Munafikun. Amma nifakul-amali (munafuncin aiki) kuwa to shi ne wanda ya zo a cikin hadisin Abdullahi dan Amr inda Annabi (S.A.Ws) yake cewa: "Dabi'u guda hudu duk wanda suka kasance tare da shi, to ya zama cikakken munafiki, wanda kuma ya ke da daya daga cikinsu to yana da dabi'ar munafukai har sai ya bar ta: idan ya yi zance ya yi karya, idan aka amince masa ya ci amana, idan ya yi alkawari ya yi yaudara, idan ya yi husuma sai ya yi fajirci". Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta: (34) da Muslim a hadisi mai lamba ta: (106). In mutum ya siffantu da daya daga cikin wadannan dabi'u guda hudu, to bai fita daga Musulunci ba, saidai yana da tawayar imani. Allah Ne Mafi sani.

Tuesday, November 28, 2023

BULAGORON MANZON ALLAH (S.A.Ws) ZUWA ƊA'IF: KASHI NA ƊAYA (01)

BULAGORON MANZON ALLAH (S.A.Ws) ZUWA ƊA'IF: KASHI NA ƊAYA (01) Bayan shekaru tara tun lokacin da Allah Ta'ala Ya fara saukan masa da wahayi, Manzon Allah (S.A.Ws), ya yi ta kokarin isar da sakon Allah Ta'ala ga mutanen Makkah, kuma ya dukufa don kokarin shiryarwa da kuma gyaran al'ummarsa. In ban da wasu 'yan kalilan da suka karbi sakon Musulunci, ko kuma suke taimaka masa ko da yake basu Musulunta ba, kusan sauran mutanen Makkah sun tashi ne haikan, wajen kokarin azabtar da Shi da kuma wulakanta Shi, tare da Sahabbansa.
Baffansa Abu Ɗalib, yana daya daga cikin mutanen kirki da suke agaza masa duk da cewar bai shiga Addinin Musulunci ba. Shekara guda bayan rasuwar Abu Ɗalib, sai Kuraishawa suka samu abin da suke so, inda suka kara tashi haikam wajen irin musgunawar da suke yi, ba tare da samun mai kwaban su ba. A can Ɗaif, wanda shi ne gari na biyu mafi girma a dukkan yankin Hijaz (watau kasar Makkah), akwai wata kabila da ake kira banu Thakif, wadanda suma masu fada a ji ne, kuma suna da 'yar dama. Don haka sai Manzon Allah (S.A.Ws) ya kama hanya zuwa garin na Ɗaif, domin kokarin shawo kansu, su shiga Musulunci, kana kuma su taimakawa Adddinin na Islama, tare da Musulmin da Kuraishawa ke ganawa ukuba, yadda a nan gaba kuma zai zama wata cibiya ko kuma sansanin yada Addinin Musulunci. Da isarsa Ɗaif, sai ya zarce (zuwa) (Jaula) ziyarar manyan hakiman garin, su uku, inda ya ziyarci ko wannensu ɗai-ɗai da ɗai-ɗai. Kana ya kira su don amsa wannan muhimmin sako na (Musulunci) da kuma bayar da tasu gudunmuwar ga Annabin Allah Ta'ala. Mai makon ma su amsa wannan gayyata da ya yi musu, MU HAƊU A KASHI NA BIYU Ya Allah kayi salati ga Annabin rahama Muhammad (S.A.Ws) *✍️*Ahmad Musa*

Tambaya NA BIYU (0002)SHIN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W.) NE FARKON HALITTA?

Tambaya NA BIYU (0002)SHIN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W.) NE FARKON HALITTA? Akwai hadisin da ya zo wanda yake nuna cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, shi ne farkon wanda aka fara halitta, sai dai hadisin bai inganta ba, wasu malaman hadisin, kamar Ibnu-kathir a tarihinsa da Albani a silsilatussahiha hadisi mai lamba (458), sun ce hadisin karya ne. Fadin cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ne farkon wanda aka halitta, ya sabawa Alkur'ani, ta bangarori da dama, ga wasu daga ciki: 1. Allah Ya tabbatar da cewa Annabi Muhammad (S.A.Ws) mutum ne kamar yadda hakan ya zo a ayoyi daban-daban, sannan kuma Allah Ya tabbatar da cewa gabadaya mutane daga Annabi Adam aka same su, kun ga idan ka ce Annabi Muhammad shi ne farkon halitta hakan ya sabawa ayoyin Alkur'anin da suka yi bayanin hakan. 2. Tarihi ya zo da bayanin nasabar Annabi Muhammad (A.A.Ws), tun daga mahaifinsa har zuwa Annabi Ibrahim, kun ga wannan yana nuna an halicce shi ne daga maniyyin mahaifinsa, kamar yadda aka halicci ragowar mutane daga hakan. Zance mafi inganci shi ne : farkon abin da Allah Ya fara halitta shi ne Al'arshi, kamar yadda ya zo a cikin Sahihi Muslim a hadisi mai lamba (2653): "Allah Ya kaddara abubuwa kafin Ya halicci sama da kasa da shekaru dubu hamsin a lokacin Al'arshinsa yana kan ruwa", Kun ga wannan yana nuna cewa Al'arshi ne farkon abin da aka fara halitta, ba Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba. Allah Ne Mafi sani.

Monday, November 27, 2023

Tambaya NA ƊAYA (1) SHIN YA HALATTA ARNIYA TA YIWA MUSULMA KITSO?

Tambaya NA ƊAYA (1) SHIN YA HALATTA ARNIYA TA YIWA MUSULMA KITSO? Ya halatta macen da ba Musulma ba ta yiwa Musulma kitso, saboda a zance mafi inganci, al'aurar mace ga 'yar'uwarta mace, shi ne daga guiwa zuwa cibiya, babu bambanci tsakanin kafira da Musulma a cikin haka, domin a zamanin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Yahudawa mata suna shiga gidan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma ba a samu suna yin shiga ta musamman ba, idan za su shigo, sai dai in kafirar ta na da wani sharri da ake jin tsoro, to wannan mace za ta iya suturta daga ita, sannan kuma mutukar akwai Musulma, to ita ta fi dacewa ayi hulda da ita. Allah Ne ma fi sani.

Saturday, March 12, 2022

AKWAI ABUBUWA DA YAKAMATA KUSANI GAMEDA AIKIN POLICE INTELLIGENCE OFFICER DA KUMA VEDEO DA AKE YAƊA WA DA SHI AKAN DCP ABBA KYARI

AKWAI ABUBUWA DA YAKAMATA KUSANI GAMEDA AIKIN POLICE INTELLIGENCE DA KUMA VEDEO DA AKE YAƊA WA AKAN DCP ABBA KYARI Hakia DCP ABBA KYARI mutum ne kamar kowa zai iya yin daidai zai iya yin akasin haka kamar yadda a fage na aikinsa zai iya yin kuskuri saboda kasancewar shi ɗan Adam ajizi, amma abin dubawa anan shin alkhirin sa ya rinjaye sharrin sa? DCP Abba Kyari shine fa wadda yayi nasarar kama Tawagogin ‘Yan ta’adda Har ‘Dari da Hamisin 150… a gurare daba-daban a kuma lokaci daban-daban, dan Allah mutambe kanmu shin DCP ABBA KYARI wani hanya yake bi har ya iya kama wa'yannan tawagogin yan ta'addan? Idan baku manta ba a shekara ta 2021 DCP ABBA KYARI ya tura kwararrun jami'an tsaro daga cikin yaransa, suka yi shiga irin na tsagerun yan ta'adda a wani gari cikin Jihar Imo a matsayin tarko na dabarun ɓadda sawu irin na INTELLIGENCE POLICE domin su kama wani kasurgumin 'dan ta'addan IPOB, kamar yadda zaku gansu a cikin hoto na farko, kuma Alhamdulillah kwalliya ta biya kuɗin sabulu
Da wannan ne yasa nake tunanin ɗaya cikin biyu zai iya faruwa gameda vedeo da ake yaɗawa gameda DCP ABBA KYARI Na farko kodai yazamana yayi aiki ne na dabarun ɓadda sawu irin na POLICE INTELLIGENCE OFFICER ko kuma anyi editing ɗin CCTV CAMERA ɗin ne aka bada shi ga hukumar NDALE saboda suyi amfani dashi gurin kama DCP ABBA KYARI domin yan ta'adda suci karensu ba babbaka, saboda akwai na'ura da dama da za'a iya amfani dasu wajen editing CCTV CAMERA kamar irin su 1. EaseUS Video Editor (Windows) 2. Video Editor (Windows) 3. HitFilm Express (Windows) 4. Davinci Resolve (Windows) 6. Avidemux (Windows) 7. Blender (Windows) 8. Lightworks (Windows) 9. Clideo Video Adjuster (Online) 10. Adobe Spark (Online) 11. Panzoid Video Editor (Online) 12. ClipChamp (Online) Waɗannan windows ɗin duk ana iya amfani dasu wajen editing vedeo a CCTV CAMERA, da wannan ne nake bawa hukumar NDALE shwara dan Allah tayi amfani da iMOVIE (MAC) saboda ta gano hakiƙanin vedeo dake CCTV CAMERA domin tabbatar da gaskiya Ya Allah kaine masanin abinda ke ɓoye ya Allah ka tabbatar mana da gaskiya kuma ka tona asirin azzalumai ✍🏻Ahmad Musa

Sunday, February 27, 2022

TARIHIN ANNABI SULAIMAN IBN DAWUD (AS) TUN DAGA FARKO HAR KARSHE (Larabci: سُلَيْمَان بْن دَاوُوْد,

TARIHIN ANNABI SULAIMAN IBN DAWUD (AS) TUN DAGA FARKO HAR KARSHE (Larabci: سُلَيْمَان بْن دَاوُوْد, Sulaymān ibn Dāwūd (Larabci: سُلَيْمَان بْن دَاوُوْد, Solomon ɗan Dawuda) ya kasance, a cikin Alƙur'ani, wani Malik (مَلِك, Sarki) da Nabī (Annabi) na Isra'ila. Hadisai na Musulunci gabaɗaya sun yarda cewa shi ne sarki na uku na yahudawa, kuma mai hikima ga al'ummar. [1] cikakkentarihin Addinin Islama yana kallon Sulemanu a matsayin ɗayan zaɓaɓɓu na Allah, wanda aka ba shi baiwar da yawa daga Allah, gami da ikon yin magana da dabbobi da aljannu. Musulmai sun ci gaba da cewa ya kasance mai aminci ga Allah makaɗaici a tsawon rayuwarsa; Ya yi mulki bisa adalci a kan Isra'ilawa duka. ya sami albarka tare da matakin Sarauta wanda ba a ba kowa a bayansa da shi ba; kuma ya cika dukkan dokokinsa, ana masa alkawarin kusanci da Allah a Aljanna a karshen rayuwarsa. Marubutan tarihi na Larabawa suna ganin Sulemanu a matsayin ɗayan manyan masu mulki a duniya. [3] Tarihi a cikin Alqur'ani Hukuncin filin A cikin labarin farko da ya shafi Sulaiman, Kur'ani (21:78) a takaice ya yi ishara da wani labari cewa, Sulaiman yana tare da mahaifinsa, lokacin da wasu mutane biyu suka zo suka nemi Dawuda ya yi hukunci a tsakaninsu game da wata kasa (حَرْث, filin) [4] Daga baya masu sharhin musulmai sun fadada wannan ishara, da suka hada da Al-Tabari, Baidawi, da Ibn Kathir. Sun ce na farkon daga cikin mutanen biyu ya ce yana da gonar inabin da ya kula sosai a cikin shekarar. Amma wata rana, lokacin da ba ya nan, tumakin mutumin ɗayan suka ɓata a cikin gonar inabin suka cinye 'ya'yan inabin. Ya nemi a biya shi diyyar wannan barnar. [8] Da jin wannan korafin na mutumin, sai sulaimanu ya ba da shawarar cewa mai garken tumakin ya dauki gonar garken na wani ya gyara tare da noma shi har sai inabin ya koma yadda yake a da, inda ya kamata ya mayar wa mai shi. A lokaci guda, mai gonar inabin zai kula da tumakin kuma ya amfana da ulu da madararsu har sai an mayar masa da ƙasarsa, a lokacin ne zai mayar da tumakin ga mai su. Matsayin hukuncin Sulemanu, wanda Kur'ani ya ce, [9] zai bayyana Sulemanu a duk rayuwarsa. Ḥikmah (Hikima), bisa ga al'adar Musulmai, koyaushe ana haɗa ta da Sulaiman, wanda daga baya ma za a kira shi Sulaimān al-Ḥakīm (سُلَيْمَان ٱلْحَكِيْم, "Sulemanu Mai hikima"). An tsara wannan labarin a cikin Kebra Nagast, amma a matsayin takaddama da ɗan Suleman ya yanke hukunci. Sarauta sarauta Lokacin da Dauda ya mutu, Sulemanu ya gaji matsayinsa na Annabin Sarkin Isra'ilawa. Ya yi addu’a ga Allah Ya ba shi Mulki wanda ba zai misaltu da irinsa ba. [10] Allah ya karɓi addu'ar Sulemanu kuma ya ba shi abin da yake so. A wannan marhala ne Sulemanu ya fara samun dimbin kyaututtuka da Allah zai ba shi tsawon rayuwarsa. Kur’ani ya ba da labarin cewa iska ta kasance karkashin Sulaiman ne, [11] kuma yana iya sarrafa ta da son ransa, kuma aljannu ma sun shiga karkashin ikon Sulaiman. Aljannu sun taimaka wajen karfafa mulkin Sulaiman, kuma kafiran cikinsu tare da Shaidan [12] aka tilasta su gina masa wuraren tarihi. [13] Allah kuma ya sa ʿayn mu'ujiza (عَي foن, 'fount' ko 'spring') na narkakken qiṭr (قِطْر, 'brass' ko 'copper') ya gudana ga Sulaiman, don aljannu su yi amfani da shi wajen aikinsu. An ma koya wa Sulemanu harsunan dabbobi iri-iri, kamar su tururuwa. Alqurani ya ba da labarin cewa, wata rana, Sulemanu da rundunarsa sun shiga wādin-naml (وَادِ ٱلْنَّمْل, kwarin tururuwa). Da ganin wani Sulaiman da rundunarsa, wata namlah (نَمْلَة, mace tururuwa) ta gargadi sauran duk cewa: “... ku shiga gidajenku, kada Sulaiman da rundunarsa su murkushe ku (a ƙafa) ba tare da kun sani ba.” [14] Nan da nan fahimta abin da tururuwa ta faɗi, Sulemanu, kamar koyaushe, ya yi addu'a ga Allah, yana gode masa da ya ba shi irin waɗannan kyaututtukan [15] kuma yana ci gaba da kaucewa taka mulkin mallaka. [16] [17] Hikimar Sulemanu, duk da haka, wata kyauta ce da Allah ya ba shi, kuma musulmai suna ci gaba da cewa Sulemanu bai taɓa mantawa da addu’arsa ta yau da kullun ba, wanda ya fi muhimmanci a gare shi fiye da kowace kyautar tasa. sulaiman Cin nasarar Saba ' nasara Wani muhimmin al'amari game da sarautar Sulemanu shi ne girman rundunarsa, wacce ta ƙunshi maza da aljannu. Sulemanu yakan bincika sojojinsa da jarumawa har da aljanu da dukan dabbobin da suke aiki a ƙarƙashinsa. Wata rana, lokacin da yake duba rundunarsa, Sulemanu ya tarar da Hud-hud (هُدْهُد, Green peafowl ko Hoopoe) sun ɓace a cikin taron. [18] Ba da daɗewa ba, duk da haka, Hud-hud ya isa kotun Sulemanu, yana cewa "Na kewaye (yankin) wanda ba ku kewaye shi ba, kuma na zo muku daga Saba 'da labari mai gaskiya." [19] The Hud-hud kara ya gaya wa Sulemanu cewa mutanen Sheba suna bautar Rana, amma matar da ta yi mulkin Masarautar tana da hankali da ƙarfi. Sulemanu, wanda ya saurara sosai, ya zaɓi rubuta wasiƙa zuwa ƙasar Sheba, ta inda zai yi ƙoƙari ya shawo kan mutanen Sheba su daina bautar Rana, kuma su zo ga bautar Allah. Sulaiman ya umarci Hud-hud da ya ba wa Sarauniyar Sheba wasikar, sannan ya buya ya lura da yadda take yi. [20] Hud-hud din ya karbi umarnin Sulaiman, ya tashi ya ba ta wasikar. Daga nan sai Sarauniyar ta kira ministocin ta a kotu ta sanar da wasikar da Sulaiman ya rubuta wa mutanen Sheba: "Da sunan Allah Mai rahama, Mai jin kai, Kada ku daukaka a kaina, amma ku zo wurina a matsayin Muslimīn (مُسْلِمِيْن). " Ta nemi shawarwari daga ministarta da gwamnatinta tana mai cewa "Ya ku mutane na, na san cewa dukkanku jarumai ne kuma jarumai, kuma babu wani a fuskar Duniya da zai iya fatattakar sojojinmu, amma duk da haka ina son ra'ayinku." Mutanen kotun sun amsa: "Kuna da dukkan iko, kuma duk umarnin da kuka bayar, zaku same mu masu biyayya." Daga ƙarshe, sai Sarauniya ta zo wurin Sulemanu, tana mai yin bushararta ga Allah. Mutuwa Kur'ani ya ba da labarin cewa Sulemanu ya mutu yayin da yake dogara ga sandarsa. Yayin da ya kasance a tsaye, ya tallafi sandarsa, aljanun sun yi tsammanin har yanzu yana raye kuma yana kula da su, don haka suka ci gaba da aiki. Sun fahimci gaskiya ne kawai lokacin da Allah ya aiko da wata halitta wacce take rarrafe daga ƙasa kuma tana cizon sandar Sulaiman har sai da jikinsa ya faɗi. Sannan Kur'ani ya yi tsokaci kan cewa da sun san gaibu, da ba su zauna cikin azabar wulakanci ba ta bayi. mutuwa A cewar Kur'ani, mutuwar Sulemanu darasi ne da za a koya: To, a l Wekacin da Muka hukunta mutuwar (Sulaiman), bãbu abin da ya nuna musu mutuwarsa sai aan ts worro na ƙasa, wanda ke taƙawa (a hankali) ga sandarsa: sab whenda haka, a l hekacin da ya faɗi, aljannu ya gani a sarari cewa, dã sun kasance sun san Ba za su zauna ba a cikin azãba mai wulãkantãwa. - Alkur'ani, Sura ta 34 (Sabaʾ), Ayah 14