Friday, January 8, 2021

SABANIN MALAMAI

 Kamar yadda aka sani, duk abinda ya taso wanda yake da alaqa damu, yake da alaka da al-ummar mu, mukan yi magana, wani lokaci maganar tayi zafi ma wasu, su fadi bakaken magana akan mu, wasu su yi magana mai kyau, toh wannan ba wani abin damuwa bane in sha Allah, dama haka mutane suke.....

Acikin satin nan anyi ta maganganu game da halacci ko haramcin sana'ar na'urar P.O.S ko (Point Of Sell) machine, wasu Malamai sunce halal ne, wasu sun ce haram ne.

.

Ni zanyi magana ne a matsayina na ordinary mutum, ni ba Malamin addini bane, amma kafin nace wani abu akai, ina so na ja hankalin al-umma, musamman 'daliban ilimi da Malaman Musulunci a Nigeriya:

Cewa dole ne mu tashi muyi karatu mai yawa game da addinin Musulunci da kuma Boko, dole ne mu dinga zurfafa bincike da karatu akan al-amuran yau da kullum kafin muyi magana da aiki.

.

Dole Malamai da 'daliban ilimi su tashi da karatu akan abubuwan zamani, Misali, zaka ga Malamai masu bayar da Fatawa basu san komai game da Online business ba, basu san Forex Trading ba, basu san Crypto currencies ba, Insurance da sauran su, wannan abin kunya ne ga addinin mu da masu ilimin mu, dole ne mu fahimci abubuwan dan mu bayar da amsar da ta dace al-Qur'ani da Sunnah ga al-umma a zamanin mu.

Dan mu fitar da Musulunci daga kunyata a wurin 'yan duniya.

.

A wannan zamanin, ilimin Boko kadai bai isa ya wadatar da mutum ba akan duniyar nan, sannan zama shiru baka san me yake gudana ba, ba zaka iya magana akan halaccin abu ko haramcin sa ba.

Abu na biyu shine, kafin kace abu Kaza halal ne, ko Haram ne, kana da bukatan Legal and Textual clear backing daga al-Qur'ani ko Hadisi.

Abin nufi, dole sai ka zamu Aya ko Hadisi karara akai, idan ba haka ba toh sai dai ka bayar da Fatawa ko kayi Qiyasi (Analytical Deduction).

.

Matsalar ba nan duniya ne abin damuwa ba, lahira gaban Allah ne matsalar, mutane nawa ne suka yi amfani da fatawar ka ko Qiyasin ka, ta yaya ka basu wannan amsar, kayi binciken da babu lalaci aciki ko kuma akwai lalaci da rashin bin diqqah, sannan fatawar ko Qiyasin dai dai ne? 

Sannan menene a zuciyar ka, mecece manufar ka game da bayar da wannan amsar? duk sai an duba wannan a gaban Allah kafin a sake mutum ya tafi wuta ko Aljannah.

.

Abu na uku shine sabanin fahimta, duk wanda yake yawan karatu ba zai dinga daga hankalin sa akan sabanin fahimta ba, saboda idan har kana karatu zaka ga abubuwan da sun fi POS rikici, da 'daure kai, wannan sabanin tun a zamanin manzon Allah da Sahabbban sa aka faro, sabani ne akan Reshe (Furu') ko Rassa, ba sabani ne akan Usul (Tushe ko Tushiya ba), simple example da zan bayar shine:

.

1. Acikin sahabban manzon Allah akwai wadanda suke fahimtar sakin mace (Divorce), saki uku a kalma 'daya ya halatta, wasu kuma sun ce a'a bai halatta ba.

Kuma har yau miliyoyin Musulmi suna kan fahimta iri iri akan wannan, yaya za kayi dasu?

Wannan matsalar ba tafi POS rikici ba? ba tafi POS 'daure kai ba? ba makawa tafi POS, dan POS lamarin sa ma kusan a fili yake.

2. Acikin Musulmi akwai wadanda suke fahimtar yin sallar tahiyyatul Masjid bayan sallar Asubah da La'asar bai halatta ba, wasu kuma suna ganin ya halatta, kuma har yau wannan sabanin yana kan gudana acikin Malamai ma tukun, ba acikin Civilians wadanda ba Malamai ba.

.

3. Wasu suna da fahimtar yin sallar Qasaru yayin koma gida daga tafiya bata halatta ba idan za'a isa gida lokacin sallar bai fita ba.

Wasu Malaman suna ganin ya halatta.

Wasu Sahabbban manzon Allah suna fahimtar yin Qasaru na tsawon kwana uku ne rak, daga nan zaka cigaba da cika sallah, wasu suna fahimtar na kwana goma ne, wasu na ganin na kwana 21 ne, wasu na ganin na tsawon watanni shida ne, daga nan sai ka fara cika sallah.

.

Acikin Malamai wasu suna ganin yaro namiji sai ya kai shekaru 15 kafin ya balaga, wasu suna cewa a'a ba sai lallai ya kai shekaru 15 ba, suna cewa sai an samu sauyi daga gabobin jikin sa, ko ya fara mafarkin mace, da sauran su.

.

Ko kasan sabanin Malamai da sahabbai game da Ar-Rajulul Mafquwd, mutumin da ya bata, ba'a gan shi ba, tsawon lokaci, yaya matar sa za tayi, tsawon yaushe zata zauna, zuwa yaushe za'a bata dama ta auri wani? 

Idan ta auri wani sai wancan ya dawo, yaya za'a yi?

.

Sahabbai kenan fa, ka isa ka zage su akan fahimtar su ga al-Qur'ani ko Hadisi? Ka isa kace masu son zuciya ne? 

Dan haka ba dai dai bane dan wane yace POS halal ne ka zarge shi, ko dan wane yace Haram ne ka zarge shi, kaje ka duba hujjojin su, duk wanda yafi karfi a wurin ka, duk wanda hujjar sa tafi karfi a zuciyar ka sai ka dauka.

Amma ba dai dai bane ka soki wadanda suka dauki fatawar da ba irin taka ba.

.

Ko san cewa Malamai suna kan tattauna halacci ko haramcin sakin mace ta sakon Text message ta waya, WhatsApp ko Facebook? ko kasan anyi sabani kuma ana kan tattauna matsayin sakin mace ta kiran waya (Phone call) yayin da Network baida kyau, bata jin sa shi kuma yana jin ta?

Abubuwan suna nan da yawa, yan uwana matasa karatu zamu tashi muyi dare da rana kafin mu iya kare wannan addinin.

.

In sha Allah, nan gaba zan yi rubutu na musamman akan fahimtar da nayi ma P.O.S, na riga na kammala bincike akai da kashi 80, kuma na samu matsaya akai, bana da wata shakka.

Abu 'daya ne banyi ba, shine har yau banji muryar Malaman da suka ce halal ne ko Haram ba, nayi bincike na ne base on ilimi na, da abinda nake dasu.

.

Amma kasancewar Malaman suna gaba damu, sun fi ilimi, sun fi mu sani, dole zanje na saurari hujjojin kowani bangare, mu tattara su, sai mu zo mu warware matsalolin 'daya bayan 'daya a nan shafin mu na Facebook in sha Allah.Kamar yadda aka sani, duk abinda ya taso wanda yake da alaqa damu, yake da alaka da al-ummar mu, mukan yi magana, wani lokaci maganar tayi zafi ma wasu, su fadi bakaken magana akan mu, wasu su yi magana mai kyau, toh wannan ba wani abin damuwa bane in sha Allah, dama haka mutane suke.....

Acikin satin nan anyi ta maganganu game da halacci ko haramcin sana'ar na'urar P.O.S ko (Point Of Sell) machine, wasu Malamai sunce halal ne, wasu sun ce haram ne.

.

Ni zanyi magana ne a matsayina na ordinary mutum, ni ba Malamin addini bane, amma kafin nace wani abu akai, ina so na ja hankalin al-umma, musamman 'daliban ilimi da Malaman Musulunci a Nigeriya:

Cewa dole ne mu tashi muyi karatu mai yawa game da addinin Musulunci da kuma Boko, dole ne mu dinga zurfafa bincike da karatu akan al-amuran yau da kullum kafin muyi magana da aiki.

.

Dole Malamai da 'daliban ilimi su tashi da karatu akan abubuwan zamani, Misali, zaka ga Malamai masu bayar da Fatawa basu san komai game da Online business ba, basu san Forex Trading ba, basu san Crypto currencies ba, Insurance da sauran su, wannan abin kunya ne ga addinin mu da masu ilimin mu, dole ne mu fahimci abubuwan dan mu bayar da amsar da ta dace al-Qur'ani da Sunnah ga al-umma a zamanin mu.

Dan mu fitar da Musulunci daga kunyata a wurin 'yan duniya.

.

A wannan zamanin, ilimin Boko kadai bai isa ya wadatar da mutum ba akan duniyar nan, sannan zama shiru baka san me yake gudana ba, ba zaka iya magana akan halaccin abu ko haramcin sa ba.

Abu na biyu shine, kafin kace abu Kaza halal ne, ko Haram ne, kana da bukatan Legal and Textual clear backing daga al-Qur'ani ko Hadisi.

Abin nufi, dole sai ka zamu Aya ko Hadisi karara akai, idan ba haka ba toh sai dai ka bayar da Fatawa ko kayi Qiyasi (Analytical Deduction).

.

Matsalar ba nan duniya ne abin damuwa ba, lahira gaban Allah ne matsalar, mutane nawa ne suka yi amfani da fatawar ka ko Qiyasin ka, ta yaya ka basu wannan amsar, kayi binciken da babu lalaci aciki ko kuma akwai lalaci da rashin bin diqqah, sannan fatawar ko Qiyasin dai dai ne? 

Sannan menene a zuciyar ka, mecece manufar ka game da bayar da wannan amsar? duk sai an duba wannan a gaban Allah kafin a sake mutum ya tafi wuta ko Aljannah.

.

Abu na uku shine sabanin fahimta, duk wanda yake yawan karatu ba zai dinga daga hankalin sa akan sabanin fahimta ba, saboda idan har kana karatu zaka ga abubuwan da sun fi POS rikici, da 'daure kai, wannan sabanin tun a zamanin manzon Allah da Sahabbban sa aka faro, sabani ne akan Reshe (Furu') ko Rassa, ba sabani ne akan Usul (Tushe ko Tushiya ba), simple example da zan bayar shine:

.

1. Acikin sahabban manzon Allah akwai wadanda suke fahimtar sakin mace (Divorce), saki uku a kalma 'daya ya halatta, wasu kuma sun ce a'a bai halatta ba.

Kuma har yau miliyoyin Musulmi suna kan fahimta iri iri akan wannan, yaya za kayi dasu?

Wannan matsalar ba tafi POS rikici ba? ba tafi POS 'daure kai ba? ba makawa tafi POS, dan POS lamarin sa ma kusan a fili yake.

2. Acikin Musulmi akwai wadanda suke fahimtar yin sallar tahiyyatul Masjid bayan sallar Asubah da La'asar bai halatta ba, wasu kuma suna ganin ya halatta, kuma har yau wannan sabanin yana kan gudana acikin Malamai ma tukun, ba acikin Civilians wadanda ba Malamai ba.

.

3. Wasu suna da fahimtar yin sallar Qasaru yayin koma gida daga tafiya bata halatta ba idan za'a isa gida lokacin sallar bai fita ba.

Wasu Malaman suna ganin ya halatta.

Wasu Sahabbban manzon Allah suna fahimtar yin Qasaru na tsawon kwana uku ne rak, daga nan zaka cigaba da cika sallah, wasu suna fahimtar na kwana goma ne, wasu na ganin na kwana 21 ne, wasu na ganin na tsawon watanni shida ne, daga nan sai ka fara cika sallah.

.

Acikin Malamai wasu suna ganin yaro namiji sai ya kai shekaru 15 kafin ya balaga, wasu suna cewa a'a ba sai lallai ya kai shekaru 15 ba, suna cewa sai an samu sauyi daga gabobin jikin sa, ko ya fara mafarkin mace, da sauran su.

.

Ko kasan sabanin Malamai da sahabbai game da Ar-Rajulul Mafquwd, mutumin da ya bata, ba'a gan shi ba, tsawon lokaci, yaya matar sa za tayi, tsawon yaushe zata zauna, zuwa yaushe za'a bata dama ta auri wani? 

Idan ta auri wani sai wancan ya dawo, yaya za'a yi?

.

Sahabbai kenan fa, ka isa ka zage su akan fahimtar su ga al-Qur'ani ko Hadisi? Ka isa kace masu son zuciya ne? 

Dan haka ba dai dai bane dan wane yace POS halal ne ka zarge shi, ko dan wane yace Haram ne ka zarge shi, kaje ka duba hujjojin su, duk wanda yafi karfi a wurin ka, duk wanda hujjar sa tafi karfi a zuciyar ka sai ka dauka.

Amma ba dai dai bane ka soki wadanda suka dauki fatawar da ba irin taka ba.

.

Ko san cewa Malamai suna kan tattauna halacci ko haramcin sakin mace ta sakon Text message ta waya, WhatsApp ko Facebook? ko kasan anyi sabani kuma ana kan tattauna matsayin sakin mace ta kiran waya (Phone call) yayin da Network baida kyau, bata jin sa shi kuma yana jin ta?

Abubuwan suna nan da yawa, yan uwana matasa karatu zamu tashi muyi dare da rana kafin mu iya kare wannan addinin.

.

In sha Allah, nan gaba zan yi rubutu na musamman akan fahimtar da nayi ma P.O.S, na riga na kammala bincike akai da kashi 80, kuma na samu matsaya akai, bana da wata shakka.

Abu 'daya ne banyi ba, shine har yau banji muryar Malaman da suka ce halal ne ko Haram ba, nayi bincike na ne base on ilimi na, da abinda nake dasu.

.

Amma kasancewar Malaman suna gaba damu, sun fi ilimi, sun fi mu sani, dole zanje na saurari hujjojin kowani bangare, mu tattara su, sai mu zo mu warware matsalolin 'daya bayan 'daya a nan shafin mu na Facebook in sha Allah.

Nagode.....

✍️

Abdul-Hadi Isah Ibrahim.

Nagode.....

✍️

Abdul-Hadi Isah Ibrahim.

Friday, December 4, 2020

KASHI NA BIYU, TATTAUNAWAR HUZAIFAH (R.A) DA MANZON ALLAH (S.A.Ws) GAMEDA FITINUN DA ZASU AUKU

Akashi na ɗaya mun tsaya a daidai inda Huzaifah (R.A) yaji amsar Annabi (S.A.Ws), sa'annan ya ƙara nuna damuwarsa ƙwarai da gaske, don haka sai ya ci gaba da irin tambayoyi na irin bala'in da za su aukamma Musulmi.

Huzaifah:  'Ya Rasulallah! Wai shin yaya za mu samu wani alherin bayan wannan masifa?'

Annabi:  'Ih, alheri zai sauka bayan wannan, toh amma sai dai cibiyoyin jama'a ba za su kai irin na da ba (ta fuskar fahimtar abubuwa na addini).

Huzaifah:  'Wata masifar kuma za ta auku bayan wannan alheri?'

Annabi:  'Ih, sai dai a wannan lokaci akwai mutanen da za su ɓatar da jama'a su jefa su wuta.'

Huzaifah:  'Me ka ga ya kamata in yi idan na iske wannan lokaci?'

Annabi:  'Idan ka taras da wata ƙungiyar Musulmi sun haɗe karkashin Amir guda to ka bi su. Idan ko ba haka ba, toh ka guji bin duk wasu 'yan ƙungiyoyi, gwamna ka koma ƙurya ko kuma ka koma gindin bishiya (watau daji) kayi ta zama a can, har mutuwa ta zo maka.'

A lokacin da Huzaifah (R.A) ke shirin barin duniya, ya yi ta kuka saboda damuwa da kuma turarradi. Jama'a suka ce da shi

    Kana kuka ne don za ka bar wannan funiyar?

Ya ce: 'A'a ba wai ina kuka ba ne saboda haka, Ina ƙaunar in mutu. Ina kuka ne saboda a halin yanzu lokacin da nake shirin ƙaura daga nan duniya ban sani ba ko Allah Ta'ala Yana farin ciki da ni ko kuma a'a.'

              Daga nan sai ya yi addu'a:

'Ya Allah! Wannan shi ne lokaci na ƙarshe a rayuwata (ta duniya). Ka san cewa a ko da yaushe ina ƙaunarka. Don haka ka albarkaci saduwa ta da kai.'

Ya Allah muma ka albarkaci saduwar mu da kai Kasa aljannar Firdausi itace mskomarmu.

*✍️Ahmad Musa

TATTAUNAWAR HUZAIFA (R.A) DA MANZON ALLAH (S.A.Ws) GAMEDA FITINTUNU DA ZASU AUKU KASHI ƊAYA

*Ahmad Musa*

Huzaifa (R.A) yana ɗaya daga cikin Sahabban da suka yi suna. Ana yi masa laƙabi da 'Mai Sanin Asiri.' Manzon Allah (S.A.Ws) ya bayyana masa dukkan sunayen munafukai, sa'annan ya shaida masa irin dukkan fitinun da za su samu Musulmi a jere tun daga lokacin har zuwa tashin ƙiyama.

Ya bayyana masa cikakken (sunan mai tada fitinar, iyayensa da kuma wurin da ya fito da sauransu) da irin abin da zai faru wanda zai shafi kusan mutane ɗari uku ko fiye da haka. Huzaifa (R.A) yana mai cewa: 'Duk sauran mutane, Kowa yakan tambayi Manzon Allah (S.A.Ws) kyawawan abubuwa, amma ni nakan yi masa tambayoyi akan abubuwa marasa kyau, yadda zan iya kare kaina daga gare su.'

Daga nan sai ya ambaci irin abin da ya gudana tsakaninsu da Manzon Allah (S.A.Ws)

Huzaifah:  'Ya Rasulallah! shin za mu koma ga sharri bayan abubuwan da ka zo mana da shi na alheri?'

Annabi:  'Ih, wani sharrin na zuwa.'

Huzaifah:  'Za mu sake samun wani alherin bayan wannan sharri?'

Annabi:  'Huzaifah! Maza tafi ka yi ta karanta Alƙur'ani, kana tunani akan ma'anarsa, sa'annan ka bi dokokin da ke cikinsa.

Wannan abu ya sa Huzaifah ya ƙara nuna damuwarsa ƙwarai da gaske, don haka sai yaci gaba da irin tambayoyi na irin bala'in da za su aukumma Musulmi.

A dakace mu zamu cigaba da bayani akan tambayoyi daya masa gameda fitintunu dazasu auku akashi na biyu insha Allahu.

Muna rokon Allah Maɗaukakin sarki ya datar damu dukkan alkhairi ya kuma kare daga dukkan sharri.

https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1

Wednesday, November 11, 2020

JAHILCI BASHI DA MADOGARA A ADDININ GASKIYA

Idan dai rubutun Larabci a jikin ƙuɗi yana nufin Musulunci ne, mai yasa ake fassara littafin Bible da yaren Larabci? Sa'annan kutambayi jahilan da suka kai ƙarar CBN cewa Kasar Israel ma Musulunci sukewa aiki? tunda ga rubutun Arabic a jikin Kuɗinsu

Batun cire rubutun Arabic akan Naira:

Idan rikicin ne muma fa mun iya, kuma muna da abin cewa, sai muce:

1. A cire hoton Cross + daga jikin motocin Ambulance na Asibitocin Nigeria, dan Nigeria ba kasar Kiristoci bane.

2. Sai muce a soke hutun ranar Asabar domin 'yan Nigeria ba Yahudawa bane.

3. Sai muce a soke hutun ranar Lahadi, domin Nigeria ba kasar Kiristoci bane.

4. Sai muce a cire kalmar "Minister" daga sunan masu taimakawa shugaban kasa, domin Ministoci ba an dana su suyi aiki ma coci bane.

Domin kalmar mukami ne a Coci.

.

5. In ba haka ba sai muce dole a saka ranar Juma'a daga cikin ranakun hutu a Nigeria, dan akwai Musulmi a kasar.

6. Indai za'a cire rubutun Arabic a jikin Naira sai muce dole a cire rubutun Hausa da Yarbanci da Igbo a jikin Naira, domin kasar ba ta Hausawa da Yarbawa da Inyamurai bane.

7. Idan ance lallai za'a cire Arabic, sai muce don me aka dauko yare biyu daga kudu (Igbo da Yoruba) aka yi rubutu dasu a jikin kudin kasar mu.

Amma aka dauko yare daya tak (Hausa) daga Arewa.

Muma Arewa dole a saka yare biyu daga Arewa.

.

8. Su an basu hutun har guda biyar:

New year.

Hutun Easter.

Hutun good Friday.

Hutun Christmas.

Hutun Boxing day.

Mu kuma an bamu guda uku rak:

Hutun babbar sallah.

Karamar sallah.

Hutun Maulidi.

.

9. Muma dole a bamu hutu har guda biyar a Nigeria.

Kuma a kara da hutun New Islamic year.

.

Ba dai tone tone suke so ba? muma fa mun iya tone tonen da yafi nasu ma.

https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1

Crédit to Abdul-Hadi Isa Abdul-Hadi Isah Ibrahim

Thursday, October 22, 2020

MABIYA JAGORAN ZAMAN LAFIYA NA DUNIYA SUNYI ABIN AYABA MUSU

Ibnul kayyim Yana cewa addini gaba dayansa kyawawan dabi'u ne, don haka duk wanda ya fika kyawawan dabi'u to ya fi ka addini.

Kyawawan dabi'u suna tsayuwa ne akan turaku guda hudu;

1. HAKURI; Wanda shi ne yake sanya mutum ya zama mai juriya da hadiye fushi, kamar yadda yake sanya tafiya sannu-a-hankali,

da rashin harzuka da kuma rashin gaggawa cikin lamura, kuma yana sanya kamewa daga cutar da wani. Kamar yadda mu yan arewa mukayi a wannan lokaci da aka gona dukiyar yan'uwanmu kuma aka ma wasu kisan gilla

2. KAMEWA: Wacce ita ce take kai mutum ga barin kaskantattun lamura, da abubuwan da ba su dace ba, ta kuma sanya shi ya zama mai kunya, wanda hakan zai sanya shi ya guji karya da rowa da annamimanci da cin naman mutane, da duk wani abu mara kyau. Kamar dai yadda aka harzuka mu domin mufita zanga-zanga amma muka kame

3. GWARZANTAKA : Wacce ita ce take kai mutum zuwa ga kare mutuncin kansa, da aikata abin da zai bashi kima, da yin kyauta ta yadda zai iya rabuwa da abin da yake so,

KUMA gwarzantaka wani abu ne da mutum zai iya rinjayar abokin gabarsa da shi, ta hanyar mallake zuciyarsa yayin fushi, kamar yadda ya zo a hadisi. Hakika mun nuna gwarzontaka a lokacin da ake cin zarafin yan'uwanmu a yankin kudu

4. Adalci; Wanda shi ne zai sanya shi ya daidaita dabi'unsa ta yadda za su zama tsaka-tsaki tsakanin ko-in-kula da wuce gona-da-iri. Kamar dai yadda muka tabbatar da ɗabianmu ta son zaman lafiya

Duk wasu dabi'u masu kyau da ka gani suna faruwa ne daga wadannan turakun guda hudu.

YA ALLAH KA BAMU KYAWAWAN DABI'U KUMA KAYI MANA MAGANIN ABINDA BAMA IYA YIWA KANMU.

https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1

HANYA MAFI SAUKI DOMIN MAGANCE KO WACE IRIN FITINA

A Zamanin Manzon Allah (S.A.Ws) Kafirai Sun Takurawa Sahabannsa da Cin zarafi da kuma kuntatawa Da Yaga Irin Halin Kunci Da Takurawar da Makiya Kafirai Da Munafukan Sukeyi Musu, Sai Yayi Musu Huduba Yace Dasu Ya Ku Jama'ar Musulmi Kuyisani Cewa Wannan Halin Da Kuke Ciki Na Musifa Bakome Bane, kuma duk abubuwan nan da suke yi muku, na karshen zamani zasu fi Muni.

Ku sani Fitina Da Bala'i Suna Nan Tafe Akarshen Zamani Idan Zamanin Yazo Zakuga Fitina Da Musifu Da Bala'o'i Sun Kunno Kai Sai Ayi Ta Addu'a Sai Bala'in Da Musifa Sunyi Kamar Sun tafi Sai Wata Musifar Da Bala'in Su Kunno Kai Wanda Sukafi Nabaya hadari.

Manzon Allah (saww) Yaci gaba da cewa Awannan Lokacin Mutane Sunrude Kai Kace Bazasu Mutuba Sun Rasa Ya Zasuyi.

Sai Yace Shawarar Da Zan bawa Al'ummata Na Wannan Zamanin Itace Su rika tunanin Ya Zanyi In cika Da Imani, Yace Duk Wanda Yariki Ya Zanyi Incika Da Imani Shine Yayi Maganin Wannan Musifar Shine Ya Kaucewa Wannan Bala'in.

Amma ba ka tsaya kana tunanin Ya wannan Musibar zata kare ba.

Abin Nufi anan shine, ka rika tunanin cewa;

Yaya Zanyi In daina Giba (Idan har kana yi).

Yaya Zanyi in daina zina (Idan har kana yi).

Yaya Zanyi In daina Sata (Idan har kanayi).

Yaya Zanyi In daina Luwadi (Idan har kana yi).

Yaya Zanyi In daina Madigo (Idan har kina yi).

Wannan Shine Tunanin da Ya kamata Mutum ya tsaya yi ba Yaya wannan Bala'in Zai kwanta ba.

Ya Allah Ina Rokon ka dan Sunayen ka Tsalkakakku Masu daraja Wayanda Muka sani da Wayanda Bamu sani ba, Ya Allah kasa Mu cika da Imani, Ya Allah ka Tsare Mu da Azabar kabari, Ya Allah kasa Aljanna ta zamo makomarmu.

https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1

Thursday, October 8, 2020

2. TAKATACCEN TARIHIN RUKAYYAH (R.Ah) YAR ANNABI (S.A.Ws)

 2. TAKATACCEN TARIHIN RUKAYYAH (R.Ah) YAR ANNABI (S.A.Ws)

An haife ta shekaru uku bayan haihuwar Zainab (R.Ah), a lokacin da Manzon (S.A.Ws) yake da shekaru 33. Ta auri Uthbah dan Abu Lahab, Baffan Annabi (S.A.Ws). To amma a lokacin tun ba su fara zama tare ba aka saukar da Surah, Al-Lahab. Abu-Lahab ya kira 'ya'yansa Uthbah da Utaibah (wanda shi ne ya auri Ummu Kulthum), har wayau, wata ' yar ta Annabi (S.A.Ws), inda ya ce da su:

Idan ba sakin 'ya'yan Muhammadu ku ka yi ba, ba zan sake kallon fuskokin ku ba.

Sun saki matan nasu. Daga baya aka ci Makkah da yaki, Uthbah ya kar6i Musulunci. RUKAYYAH (R.Ah) bayan wannan saki ta auri Sayyadina Uthman (R.A). Mijin da matar sun yi Hijirah zuwa Habasha har sau biyu.

Tun lokacin da Annabi (S.A.Ws) ya shaida wa Sahabai cewar yana sa ran ya samu umarni daga wajen Allah Ta'ala na yin Hijirah zuwa Madinah, sai suka fara matsawa zuwa can tun kafin Annabi (S.A.Ws) ya yi Hijirasa. Uthman (R.A) da Rukayyah (R.Ah) sun kuma yi Hijirah zuwa Madinah kafin Annabi (S.A.Ws) ya isa garin.

A lokacin yakin Badr, Rukayyah ba ta da Lafiya (wanda ta cika sanadin wannan cuta). Don haka sai Annabi (S.A.Ws) ya bukaci shi Uthman (R.A) ya ci gaba da zama a Madinah don lura da ita. An samu labarin irin nasarar da aka samu a yakin Badr a can Madinah yayin da jama'a ke komowa daga jana'izar Rukayyah. Don haka da Annabi (S.A.Ws) bai samu damar halartar jana'izarta ba.

Rukayyah (R.Ah) ta haifi da a lokacin da suke Habasha. An sa masa suna Abdullah, kuma yana raye mahaifiyar ta rasu, ko da yake shima ya rasu a shekara ta 4, bayan Hijirah. A lokacin yana da shekara 6.

Insha Allahu rubutu na gaba akan Ummu Kulthum (R.Ah) yar Annabi (S.A.Ws) amma kafin nan zan daniyi rubutu akan dan Ahmad Deedat saboda ya samu rauni a safiyar yau.

Muna kuma rokon Allah Ta'ala ya gafarta mana kurakuranmu ya kuma sa Aljannar Firdausi itace makomarMu baki daya. Aameen.