Tuesday, March 10, 2020

TARIHIN ANNABI SULAIMAN(A.S)....3..

 Allah Ubangiji(S.W.T)ya ce:-(KUMA SULAIMAN YA GAJI DAUDA)suratun namli.
    Abin nufi anan shine ya gaji Annabtar sa, da hikimar sa, da ilmin sa, Duk da cewa Annabi Dauda(A.S)yana da 'ya'ya goma sha tara(19).
      MU'KATIL yace:- Annabi sulaiman(A.S)ya kasance akan mulki mafi girma ga na mahaifinsa Annabi Dauda(A.S)da kuma iya hukunci, shi dai Annabi Dauda(A.S)ya kasance mai yawan ibada ne akan d'ansa Annabi sulaiman(A.S), kuma Allah (S.W.T)ya bashi mulki da hikima yana 'Dan shekara goma sha uku(13),Shima yana daga cikin mutum hud'u wad'anda suka mulki duniya gaba d'aya.
     Annabi sulaiman(A.S)ya kasance fari kuma mai jiki mai haske,kuma kyakkyawa, mai yawan gashi,yana sa fararen tufafi, kuma ya kasance mai yawan tsoran Allah(S.W.T) kuma mai tawadhi'u yana cud'anya da miskinai, kuma yana zama dasu, yana cewa miskini ya zauna da maikinai.
       Mahaifinsa Annabi Dauda(A.S)ya kasance yana shawara da shi a lokacin mulkinsa akan al'amura masu yawa, duk da cewa 'karami mai 'kananan shekaru, amma yana da cikakkyan hankali da ilmi.
          Allah Ubangiji(S.W.T)ya ke'benci Annabin sa Annabi sulaiman(A.S)da wasu darajoji da kuma kyaututtuka na baiwa, Ubangiji yana cewa:-
(HAKIKA MUN BAI WA DAUDA DA SULAIMAN ILMI, KUMA SUKA CE GODIYA TA TABBATA GA ALLAH,WANDA YA FIFI TA MU AKAN MAFI YAWA DAGA BAYINSA MUMINAI.)suratun namli;
     Kuma Ubangiji ya fad'a acikin Al'kur'ani mai girma tana mai bada labari akan Annabi sulaiman(A.S):-
YACE"YA UBANGIJI:KA GAFARTA MINI, KUMA KA BANI MULKI WANDA BAI KAMATA GA KOWA BA BAYANA".
"LALLAI KAI NE MAI YAWUN KYAUTA".
      Annabi sulaiman(A.S)yayi wannan addu'a ne Domin kada wani yayi alfahari da sarauta a bayansa, Ya halaka kuma ya halakar da wani,saboda sarauta itace asalin girman kai da alfahari.
      sai Allah ya amsa addu'ar sa ya kuma girmamashi da wasu abubuwa wanda Allah bai ta'ba horewa wani su ba, daga cikin hakittar sa ba kafin Annabi sulaiman(A.S)daga cikin hotewar da Allah(S.W.T)yayi masa daga iska, Ubangiji mad'aukakin sarki yana cewa:-
"SABODA HAKA MUKA HORE MASA ISKA TANA GUDU DA UMARNINSA, TANA TASHI DA SAUKI,INDA YA NUFA."Suratu..
       Malamai suka ce an hore masa iska a matsayin dawakan da ya yanka domin Allah, Saboda Annabi sulaiman(A.S)ya yanka dawakan ne saboda kallonsu ya hana shi sallah, wacce ita sallar farillace ta dole a kansa, amma tattalin kayan ya'ki farillace ta wani zai iya d'aukewa wani.
    sannan kuma an hore masa Aljanu domin niyyarsa ta samun 'ya'ya masu jihadi domin Allah.
     Malam muhammad Dan Is'hak yace, Annabi sulaiman(A.S)ya kasance mutum ne mai yawan ya'ki Baya iya zama ba tare da ana gwabza ya'ki ba,dan baya iya jin d'uriyar wani sarki a sassan duniya,face sai ya ya'ke shi, kuma ya nuna masa karfin mulki sa, Ya kasance idan yayi nufin ya'ki yana sa askarawansa su 'kera masa wani abu kamar girji na katako sannan sai a d'ora masa gadonsa akai sannan duk sauran jama'a da dabbobi su hau a kuma zuba kayan ya'ki kala-kala akai, bayan an gama shirya komai sai ya umarci iska ta d'aukeshi zuwa inda ya nufa,  an ce suna yin tafiyar wata a yammaci d'aya, kuma suna yin tafiyar wata a safiya d'aya, tana tana tafiya da shi duk inda ya so, shine fad'in Ubangiji(S.W.T):-
"KUMA GA SULAIMAN, MUN HORE MASA ISKA,TAFIYARTA TA SAFIYA DAIDAI DA WATA,KUMA TA YAMMA DAIDAI DA WATA."Suratu sabi'i.

......Zanci gaba insha Allahu

JUMA@ KAREEM..
 RAMADHAN KAREEM..

MUNSHA RUWA LAFIYA.

TARIHIN ANNABI SULAIMAN(A.S)...2

Sai Annabi Dauda(A.S)ya tashi ya hau kan mumbari ya yiwa Allah(S.W.T)godiya yayi yabo agareshi, sannan yace Allah(S.W.T)ya umarce ni da in khakifantar muku da Annabi sulaiman(A.S), sai Banu isra'ila suka fusata suka ce wannan yaron mai 'Karancin shekaru za'a khakifantar mana al hali a cikinmu akwai wad'anda suka fishi d'aukaka da ilmi?
        sai Annabi Dauda(A.S)yaji abinda suke fad'a sai ya kirawo manya-manyansu yace dasu naji abinda kuke fad'a, To amma kowa ya zo min da sandar sa duk wanda sandar sa tayi tsiro to shine zai zama khakifa a bayana, sai sukace sun yadda, sai kowa yaje ya kawo sandar sa, sai Annabi Dauda(A.S)yace kowa ya rubuta sunan sa a jikin sandar sa, sai duk suka rubuta sunayansa.
     sai Annabi sulaiman(A,S)ya zo da sandar sa ya rubuta sunansa shima a jikin ta, sai aka sa sandunan ackin wani d'aki aka kulle 'kofar aka datse da mukulli, aka kuma sa masu dagi daga cikin manyan shuwagaban nin su.
      Bayan asuba tayi Annabi Dauda(A,S)yayi sallar Asuba da su, Gari kuma ya waye, sai aka bud'e wannan d'akin aka fito da wad'annan sanduna kamar yadda suke, Amma sandar Annabi sulaiman(A,S)sai  akaga tuni tayi ganye kuma tayi 'ya'ya.
     sai sukace kai mun mi'kawa Annabi Dauda(A,S) wannan al'amarin, Da Annabi Dauda(A,S)sai ya godewa Allah(S.W.T,) sai ya d'ora Annabi sulaiman(A.S)a kusa da shi, sai yace da Bani isra'ila wannan shine khalifanku a baya na.
     Wahabu d'an munabbahu yace:- lokacin da Annabi Dauda(A.S)ya khalifantar da d'ansa Annabi sulaiman(A.S)ya yi masa wa'azi da cewa:-
            Ya kai 'karamin 'Da na kashedinka da fushi, domin fushi yana wulakanta ma'abocin sa, sannan kaji tsoran Allah(S.W.T)da kuma biyayya a gareshi,domin suna rinjayar ko wane irin abu ne, kada kuma ka yawaita kishi ga mutananka ba tare da wani abu ba,Domin hakan yana gadar da mummunan zato ga mutane koda kuwa ku'butattune, ka yanke kwad'ayi ga abin hannun mutane , Domin hakan wadata ce, kuma kada ka yi kwad'ayi domin shi talauci ne mahalarci, kuma kashedinka da fad'ar abinda zai yi maka wahalar cikawa da kuma abinda zai yi maka wahalar aikatawa, ka kuma tsaida kanka da harshen ka akan gaskiya, ka kuma lazamci kyautatawa, idan kuma kana da ikon Alkhairinka na yau zaifi na yau zaifi na jiya to ka aikata, ka kuma yi sallah irin sallar mai ban kwana, kamar bazaka kai gobe ba, kada kuma ka zauna da wawaye,kada kuma ka gayawa malami mummunar magana, kada kuma kayi jayayya da shi akan addani,idan kuma kayi fushi to ka zauna, kuma ka canja guri, ka 'kaunaci rahamar Ubangiji, domin rahamar Ubangiji ta yalwaci komai.
        sannan ance lokacin da aka khalifantar da Annabi sulaiman(A.S)sai ya 'Boye al'amuran sa, ya kuma auri wata mace, ya kuma 'Buya ga mutane, ya fuskanci ilmi da kuma ibada, wata rana wannan matar tasa take cewa bata taba ganin mutum mai kyawun d'abi'u irin saba, kuma mai dad'in 'kamshi ba........

zanci gaba insha Allah

musha ruwa lpy..

TARIHIN ANNABI SULAIMAN (A.S)..1..

  Annabi sulaiman(A.S)shine 'dan Annabi Dauda(A.S)Abu Huraira(R.A)ya ce Allah ya saukarwa da Annabi Dauda(A.S)littafi wanda yake dauke da Tambayoyi guda goma sha uku(13),sai Allah(S.W.T)yayiwa Annabi Dauda(A.S)wahayi akan ya Tambayi 'dan sa Annabi sulaiman(A.S)wannan Tambayoyi guda goma sha uku(13), in ya amsa su to shine Khalifa a bayan sa.

     Sai Annabi Dauda(A.S)ya kirawo malaman Bani Isra'ila guda (70)da kuma masu yawan Bauta a cikinsu, suma guda saba'in(70) sai ya zaunar da Annabi Sulaiman(A.S) a gabansu, sai yace:-ya kai 'karamin dana ha'ki'ka Ubangiji ya saukar min da wani littafi daga sama acikinsa akwai Tambayoyi , ya kuma Umarce ni da in yi maka Tambaya akansu, idan ka amsa su to kaine khalifa a baya na, sai Annabi sulaiman(A.S)ya ce:-To! Annabi zai yi min Tambaya akan abinda aka bayyana masa , amma Dogarona yana ga Allah (S.W.T).
       Sai Annabi Dauda(A.S)yace ya kai d'an 'karamin 'dana:-
menene yafi ko wane abu kusanci kuma
menene yafi kowane abu nisa?
menene  kuma yafi  'debe kewa ga Al'amura
menene kuma yafi muni ga Al'amura?
menene yafi kyau ga sauran abubuwa
menene kuma yafi muni ga sauran abubuwa?
menene yafi 'kankanta ga abubuwa
kuma menene yafi yawa ga sauran abubuwa?
kuma wanne abubuwa ne guda biyu a tsaye
wanne abubuwa ne guda biyu suke kai kawo?
kuma wanne abubuwane guda biyu sukayi Tarayya kuma wane abubuwa ne guda biyu ma'kiyan juna?
kuma wane abune idan mutum ya haushi za'a gode masa 'karshen sa, kuma wane abune idan mutum ya haushi za'a zarge shi a 'karshen sa?

   Sai Annabi sulaiman(A.S)ya ce:-Abin da yafi kowa ne abu kusanci itace lahira, Abinda yafi kuma kowanne abu nisa kuwa shine abinda ya tsere maka daga duniya.
  Abun kuma da yafi 'debe kewa ga Al'amura abin da yake sujjada a tare da shi akwai rai, abin da yafi kowane abu muni shine abinda yayi sujjada babu rai a tare da shi.
    Abu mafi kyawun sauran bubuwa kuwa shine imani bayan kafirci, mafi munin abubuwa kuma shine kafirci bayan imani.Abu mafi 'kankanta kuwa shine ya'kini.
   Abu mafi yawa ga sauran abubuwa kuma shine kokwanto.
   Abubuwa biyu da suke tsaye sune kasa da sama, wadanda suke kaikawo sune rana da wata.
    Abubuwan da sukayi tarayya ga juna sune dare da rana, ma'kiya ga juna kuma sune mutuwa da rayuwa.
   Al'amarin da idan ka haushi kuma za'a gode maka a 'karshen sa shine Ha'kuri lokacin fushi, wanda kuma za'a zarge ka a 'karshen sa shine Hukunci lokacin fushi.

   Sai Annabi sulaiman(A.S)yace wannan shine jawabin wannan Tambayoyi dai dai yadda aka saukar daga sama.
   Sai wad'annan malaman Bani Isra'ila da kuma masu yawan Bautar a cikin su suka ce Basu yadda ba har sai suma sunyi masa wata Tambaya, idan ya amsa sun yadda da shine khalifa, sai Annabi sulaiman(A.S)ya ce:-ku tambaye ni ni dai dogarona shine Allah(S.W.T).
   Sai sukace da shi, wane abune idan ya gyaru dukkan jiki ya gyaru, idan kuma ya 'Baci dukkan jiki ya 'Baci? sai yace Zuciya..........zanci gaba. insha Allahu.

  Allah ya gyara mana zuciyarmu.
Asha ruwa lpy.

Monday, March 9, 2020

KABARI LAMBUNE DAGA ALJANNAH KO KUMA RAMI DAGA JAHANNAMA

Ba wani yini da zai shude,face kabari ya yi shela, ya ce, 'Ni ne gida na daji, ni ne gidan kadaici, ni ne gidan tsutsotsi da ƙwari.'

Yayin da aka binne mumini a cikin ƙabari, ƙabarin zai yi misa maraba, yana cewa, 'Maraba da zuwan ka nan, ka kyauta da ka zo nan. A cikin dukkan masu tafiya bisa bayan ƙasa, kai ne na fi so. A yanzu da aka kawo ka zuwa gare ni. za ka ga mafi kyawun hali na'

Daga nan sai ƙabari ya yi fadi, kwatankwacin iyakar ganin mutum, sai a bude kofar Aljannah a cikin sa. Ta cikin wannan kofar, iska mai kanshin turaren Aljannah za ta dinga zuwa gareshi.'

Amma idan aka binne kafiri ko mai ƙetare iyakokin Allah Ta'ala, ƙabari zai ce, 'Ba na maraba da zuwan ka nan, kuma zuwan ka abin kyama ne. Da ba ka zo nan ba, da ya fi maka. Daga cikin dukkan masu tafiya a bisa doron ƙasa, kai ne na fi ƙi. A halin yanzu an kawo ka zuwa gare ni, kuma za ka ga irin aiki na'

Daga nan sai ya matse shi da tsakanin gaske, har sai hakarƙarinsa sun sarke da juna kamar yadda yatsun hannuwa biyu suke kurɗawa a tsakanin juna. Daga nan sai a sako masa kumurci casa'in ko casa'in da tara, za su ci gaba da yagar sa har zuwa tashin Alkiyamah.

Da daya daga cikin kumurcin zai huro dafin sa a bisa doron ƙasa, da ba wata ciyawa da za ta sake tsiro wa a kanta, har tashin Alkiyamah. Daga nan sai Manzon Allah (S.A.Ws) ya ci gaba da cewa, 'Ƙabari lambu ne daga Aljannah ko kuma rami daga Jhannama.

Ya Allah ka kare mu daga azabtar Kabari kasa Aljannar Firdausi itace makomarmu. Ãmīn ya Qādiyal Hājah~ ahmadmusainc.blogspot.com

Sunday, March 8, 2020

TUNDA ANNABAWAN ALLAH SUKA MUTU KOWA MA SAI YA DANDANAWA MUTUWA.

Annabi Suleiman Yana cikin Mutane Hudu da Suka Mulki Duniya baki daya.

BIN ABBAS (rta) Yace; Annabi Suleiman (As) ya kasan ce Kullum yana shiga BAITUL-MUKADDAS da kayan abincinsa dana sha, bai da aikinyi a ciki sai Bautar Allah (swt).

Kullum Annabi Suleiman ya shiga BAITUL-MUKADDIS, sai yaga wani abin mamaki, abin mamakin kuwa, duk lokacin da ya wayi gari a cikin Wannan Masallachin, sai yaga wata Bishiya ta fito, duk lokacin da wannan bishiya ta fito, sai shi kuma ya tambaye ta, shin ko me yasa ta fito? Kuma menene amfanin ta? To idan yaji bata da wani amfani sai ya cire ta, idan kuwa yaji tana da amfani sai yasa a cire ta a dasa a wani wuri, idan kuwa yaji ta maganice sai ya sa a rubuta irin maganin da take a bar ta a wurin.

Wata Rana yana Sallah sai wata bishiya ta tsiro a gaban sa bayan ya gama sallah sai ya tambaye ta? Sai tace Sunan ta kHARNUBATU, sai yace saboda me aka tsirar da ke? Sai tace, saboda rushe Wannan Masallachin, sai yace, ai Allah bazai rushe wannan Masallachi ba matukar ina raye, ke dai kina so ki nuna min cewa qarshen Rayuwa ta ne ya zo, sai ya cire ta ya dasa ta a wani kango, sannan ya ce; YA ALLAH INA ROKONKA KA MAKANTAR DA ALJANNU KADA SUGA MUTUWA TA, DAN MUTANE SUSAN CEWA ALJANNU BASUSAN GAIBU BA, DOMIN SUNA GAYAWA MUTANE CEWA SUN SAN GAIBU, HAR SUNA CEWA SUN SAN ABINDA ZAI FARU GOBE.

Sai Annabi Suleiman (As) ya tashi ya shiga cikin wajen da yake ibada, ya fara salla yana dogare da sandarsa, sai Allah (swt) ya dauki Ransa a wannan hali, Sai da Annabi Suleiman (As) ya shekara a macce, babu wani shaidani da ya san halin da yake ciki.

Shine fadin Allah (swt) a cikin Qur'ani; YAYIN DA MUKA HUKUNTA MUTUWA GA ANNABI SULEIMAN YA ZAMA YANA DOGARE AKAN SANDARSA, SHEKARA GUDA ALJANNU SUNA TA AIKACE-AIKACE MASU WUYA, BASU SAN YA MUTU BA, HAR SAI DA GARA TA CINYE SANDARSA YA FADI YANA MATACCE, LOKACINDA YA FADI YANA MATACCE SAI ALJANNU SUKA TABBATA CEWA SU DA SUNKASANCE SUN SAN GAIBU, DA BASU ZAMA A CIKIN WAHALA MAI WULAQANTARWA BA. (Suratul saba'I )

Dama kafin Annabi Suleiman (As) ya shiga wajen ibada sai da ya saka Aljannu aiki, wasu share-share wasu dibar zinari da a zurfa, da sauran ayukkan da yake saka su.

KU DUBA FA BABANSA ANNABI NE KA KANSA ANNABI NE SHIMA ANNABI NE.

KU DUBA FA DUKA-DUKA SHEKARA 53 YAYI A DUNIYA SHE KARUN MULKIN SA KUWA SHEKARA 40 YAYI A SAMAN MULKI.

KU DUBA FA ALLAH YA BASHI MULKI DA HIKIMA YANA DAN SHEKARA GOMA SHA UKKU, domin yana dan shekara sha uku Annabi Dawud (As) ya taba yin shari'a yace ba haka ya kamata ayi ta ba aka umurce shi da yayi shari'ar da kuma yayi shari'ar tayi dai-dai.

KU DUBA FA SHI DUNIYA GABA DAYAN TA YA MULKA.

KU DUBA FA IRIN YANDA YAKE SON TALAKKAWA HAR YA KASANCE YANA ZAMA CIKIN SU, suna Fira.

KU DUBA FA IRIN BAIWA DA KUMA ABUBUWAN DA AKA HORE MASA,

Yana umurtar Iska ta kai shi duk in da yake buqata, itace matsayin dawaki, mota, rakumin sa.

KU DUBA IRIN KARFIN MULKIN SA, ALLAH YA HORE MASA MAYAQA KUSAN MILION DARI,

Kashi ashirin da biyar (25) mutane ne, kashi ashirin da biyar(25) daga ciki Aljannu ne, kashi Ashirin da biyar (25) kwarine, kashi Ashirin da biyar (25) tsuntsayene.

KU DUBA IRIN BAIWAR DA ALLAH YA BASHI YANA JIN MAGANAR KO WANE TSUNTSU DA DABBA.

KU DUBA FA IRIN QARFI, DA IZZAR DA ALLAH (swt) YA BASHI MALA'IKA AKA BASHI DUK ALJANIN DA YA SA AIKI IDAN ALJANIN YAQI YI KO YA SABA MASA MALA'IKA YAYI MASA BULALA.

AMMA DUK WAYANNAN ABUBUWAN BASU SA AMBAR SHI A DUNIYA BA SAI DA YA MUTU KUMA A MIZANE GUDA ZA'A YI AWON LADARMU DA ZUNUBBAN MU.

Ya Allah kasa mu mutu muna masu Imani, kasa muyi Qarshe mai kyau ka sa Aljanna ta zamo makomar mu. ~Zauren fatawa

Friday, March 6, 2020

SAI ANNABI DAWUD (As) YACE; WALLAHI SUN ISHE NI.

Annabi Dawuda (As) Ya kasance Yanada masu gadinsa sun kai kimanin DUBU talatin 30,000.

Yana da wata Mata a gidan sa mai lura da duk wani abu da yake kai kawo a cikin gidan, kuma ita ce take kulle dukkan kofofin Gidan idan dare yayi, Sannan Sai ta kaiwa Annabi Dawud (AS) Makullan, sai itama ta je ta kwanta.

Wata Rana bayan ta gama aikinta zata tafi ta kwanta, sai kawai taga Wani Mutum a cikin takiyar gidan, tana ganin sa sai tace da shi, KAI WANNAN BAWAN ALLAH MAI YA KAWO KA NAN GIDAN? BA KA SAN CEWA SHI MAI GIDANNAN YANA DA TSANANIN KISHI BA, DON HAKA KAYI MAZA KA BAR WANNAN GIDA.

Yana jin haka sai yace mata; NINE NAKE SHIGA CIKIN GIDAJEN MASU MULKI BA TARE DA NEMAN IZNIN SU BA, to a lokacin da suke Wannan Magana Annabi DAWUD (As) yana tsaye yana Salla jin haka sai ya firgita ya daka tar da Sallar yace wa Wannan Matar ta shigo da shi wajensa.

To da suka Shiga Sai Annabi Dawud (As) yace da shi, MAI YA SHIGO DA KAI WANNAN GIDAN A WANNAN LOKACI BA TARE DA NEMAN IZNI BA? Sai Yace wa Annabi Dawud (As); NINE MAI SHIGA GIDAN MASU MULKI BA TARE DA WANI NEMAN IZNI BA, da Annabi Dawud (As) yaji haka Sai Yace masa, ko kaine MALA'IKAN MUTUWA? Sai Yace wa Annabi Dawud (As) Na'am, Sai Annabi Dawud (As) Yace Masa Shin kazo ZIYARA ko DAUKAR RAI? Sai Yace wa Annabi Dawud (As) nazo DAUKAR RAI ne.

Da Annabi Dawud (As) Yaji haka sai yace masa, MAI YASA BAKA SANAR DANI TUN KAFIN WANNAN LOKACI BA DOMIN IN SHIRYA? Sai Yacewa Annabi Dawud (As) Wanne Tunasar da kai Zanyi bayan duk ga alamominan da suka wuce, sai Annabi Dawud (As) yace masa Wace tunasarwa ka aiko kafin kazo? Sai Mala'ikan Mutuwa Yace masa; YA DAWUD INA MAHAIFINKA ISHA, INA MAHAIFIYARKA, INA 'YAN UWANKA, INA MAKOFTANKA, INA ABOKANKA WANE DA WANE? Sai Annabi Dawud (As) Yace duk Sun MUTU, Sai Mala'ikan Mutuwa yace masa, to duk wadannan basu isheka tunasarwa ba?

Sai Annabi Dawud (As) Yace; Wallahi sun Ishe NI.

KU DUBA FA TSAWON MULKIN ANNABI DAWUD (AS) SHEKARA ARBA'IN YANA SARAUTA KUMA SHI ANNABI NE.

KU DUBA FA IRIN DADIN MURYAR DA ALLAH (swt) YABAWA ANNABI DAWUD (AS) WANDA BAI TABA BAWA WANI DAGA CIKIN HALITTUNSA BA, Akan Dadin Muryarsa Idan Yana karatun ZABBURA Dadin MuryarSa tana sa Wanda ya Suma ya farfado da ga Suman da yake.

KU DUBA FA DAGA CIKIN BAIWAR DA ALLAH YA YI MASA YANA DA WATA SARKA DOMIN YA GANE MAI GASKIYA DA MAI QARYA A LOKACIN SHARI'A

KU DUBA FA IRIN IBADAR SA YAKANYI AZUMI YAYI YAU GOBE BAI YI HAKA YAKE KULLUM, SANNAN DAREN SA IDAN YA YI BACCI RABI YAYI IBADA A RABI.

KU DUBA FA IRIN KARFIN DA ALLAH (SWT) YA BAWA MULKINSA BABU WATA KASA DA ZAI TUNKARA BA TARE DA YACI TA DA YAQI BA.

Ya Allah kasa Idan tamu tazo ta Riskimu muna masu Imani kuma ka sa Aljanna ta zamo makomar mu a gobe Qiyama. ~Zauren Fatawa