Thursday, November 11, 2021
FALALAR RANAR JUMA'A
FALALAR RANAR JUMU'AH
Idan Allah Ya baka ikon karantawa daure kayi share domin duka mu amfana.
An karbo daga Aus ibn Aus (RA) Annabi (Saww) Ya ce, "Wanda ya yi wanki, ya yi wanka, ya matsa kusa, ya yi sammako, ya kusanto liman ya saurari huduba a ranar jumu'a, zai sami ladan tsayuwar shekara daya da azuminta da dukkan tako da ya yi. (Imamu Tirmiziy da Nasa'i suka rawaito shi).
Haka Kuma an karbo hadisi daga Anas (RA) ya ce, An bijiro da sallar Juma'a ga Manzon Allah (saww).
Mala'ika Jibrilu ne ya zo masa da ita a tafinsa kamar farin adubi, a tsakiyarsa akwai wani baqin digo, sai ya ce: "Menene wannan ya jibrilu?" Ya ce masa, "Wannan ita ce Juma'a Ubangijinka yake bijiro da ita a gare ka; domin ta kasance idi a gareka da alummarka a bayanka, kuma ku kuna da alheri a cikinta, wanda kai ne za ka zama na farkon samunsa, kuma yahuduwa da nasara su zama a bayanka. Kuma a cikinta akwai wata sa'a babu wani bawa da zai yi addu'a a cikinta ta alheri da yake rabonsa ne, face an ba shi, ko ya nemi tsari daga sharri face an ije masa mafi girma daga abin da ya nema, kuma mu a sama muna ambatonsa ranar qari.
(Dabarani ne ya rawaito shi a cikin Al-Ausat da isnadi mai kyau).
Hakika wannan falaloli ne masu girma da kyawo, muna rokon Allah ya datar damu wayannan Falalolin.