SHAWARORI ZUWA GA MASU CIKI
******************************
Wayannan shawarori zasu amfani mata masu ciki sosai da sosai ta 'bangaren lafiyarki da jaririnki tare kuma da fatan samun na tsatstsen yaro.
YA KAMATA MUSAN WANNAN KAFIN AURE SABODA LAFIYAR IYALI DA KWANCIYAR HANKALIN MU
Akwai cutuka da ya kamata a yi gwajin jini akansu a tsarin Musulunci bisa koyarwar Manzon Allah (S.A.Ws), kamar yadda yace "Babu cuta babu cutarwa a komai"
Mu sani idan har bincike a tsakanin ma'aurata ya halatta, to a yi bincike akan lafiyar ma'aurata shi ne ya fi cancanta domin sai da lafiya ne zaman auren zai inganta.
Jikin kowane 'dan adam yana dauke da wani abu da ake kira Genotype a turance. To wannan Genotype din idan har ya kasance na miji da mace su zo ɗaya to kuwa 'ya'yansu duka zasu kasance ba masu cikakkiyar lafiya ba.
Akwai → AA wannan shine lafiyayye
Akwai → AS wannan shine ke da rabin cutar (ma'ana bai munana ba).
Akwai → SS To wannan shine mai cikakkiyar cutar ta amosanin jini.
A lokacin duk lokacin da akayi aure tsakanin mai SS da SS to duka ’ya’yansu su gaji wannan nakasu (ma'ana zasu kasance masu dauke da ɗaya daga cikin cutar Gado kamar Sikila, kansar Jini, Hauka ko Gaula, cutar kuturta, da cutar Haka-Haka ). Su dukansu da ’ya’yan nasu kuma kullum sukan kasance a cikin rashin lafiya, kenan rabin zaman auren za'a iya yinsa a jinyace.
A lokacin da mai ciwon (SS) ya auri mai rabin ciwon (AS), zai iya kasancewa wasu a cikin ’ya’yansu su gaji wannan ciwo.
Amma idan mai rabin ciwon (AS) ya auri wata mai rabin ciwon (AS), to rabin ’ya’yansu ne za su iya kasancewa masu amosanin jini, sauran kuma
lafiyayyu.
Duk lokacin da mai AA ya auri mai SS Ko AS to za'a iya samun sauqi kwarai da gaske.
Amma Idan Mai (AA) ya auri mai (AA) to fa shikenan babu zance haduwa da 'ya'ya masu dauke da cutar ta Amosanin jini (Gado).
Wannan cutar Gado ( kamar Sikila, kansar Jini, Hauka ko Gaula, cutar kuturta, da cutar Haka-Haka ) suna rayuwa ne a cikin jinin mutum bil adama, cutar ana haihuwar mutum da ita ne, ma'ana cutace da ke zaune a cikin jinin jikin dan Adam.
Saboda cuta ce da ke kama jajayen kwayoyin halittu na jini. Wannan ciwo ba kwayoyin cuta ke kawo shi ba, gadonsa ake yi daga wajen iyaye, waɗan da ke da wannan nakasar a kwayoyin jini.
Wasu mutanen, nakasar tasu rabi ce, waɗanda ake wa lakabi da AS; wasu kuma duk kwayoyin a nakashe suke, waɗanda su ne a ke kira da SS.
Misali kamar cutar Sikila na daga cikin jerin ciwukan da sai dole an gada daga wurin mahaifiya da mahaifi sa’annan yake nunawa.
Insha Allahu rubutu nagaba zanyi akan YADDA AKE GANE CUTAR GADO (kamar Sikila, kansar Jini, Hauka ko Gaula, cutar kuturta, da cutar Haka-Haka )
Muna rokon ALLAH ya bamu lafiya da zama lafiya da abinda lafiya zata ci. Āmin
✍️
Ahmad Musa
https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1