Friday, December 4, 2020

KASHI NA BIYU, TATTAUNAWAR HUZAIFAH (R.A) DA MANZON ALLAH (S.A.Ws) GAMEDA FITINUN DA ZASU AUKU

Akashi na ɗaya mun tsaya a daidai inda Huzaifah (R.A) yaji amsar Annabi (S.A.Ws), sa'annan ya ƙara nuna damuwarsa ƙwarai da gaske, don haka sai ya ci gaba da irin tambayoyi na irin bala'in da za su aukamma Musulmi.


Huzaifah:  'Ya Rasulallah! Wai shin yaya za mu samu wani alherin bayan wannan masifa?'


Annabi:  'Ih, alheri zai sauka bayan wannan, toh amma sai dai cibiyoyin jama'a ba za su kai irin na da ba (ta fuskar fahimtar abubuwa na addini).


Huzaifah:  'Wata masifar kuma za ta auku bayan wannan alheri?'

Annabi:  'Ih, sai dai a wannan lokaci akwai mutanen da za su ɓatar da jama'a su jefa su wuta.'


Huzaifah:  'Me ka ga ya kamata in yi idan na iske wannan lokaci?'


Annabi:  'Idan ka taras da wata ƙungiyar Musulmi sun haɗe karkashin Amir guda to ka bi su. Idan ko ba haka ba, toh ka guji bin duk wasu 'yan ƙungiyoyi, gwamna ka koma ƙurya ko kuma ka koma gindin bishiya (watau daji) kayi ta zama a can, har mutuwa ta zo maka.'


A lokacin da Huzaifah (R.A) ke shirin barin duniya, ya yi ta kuka saboda damuwa da kuma turarradi. Jama'a suka ce da shi


    Kana kuka ne don za ka bar wannan funiyar?


Ya ce: 'A'a ba wai ina kuka ba ne saboda haka, Ina ƙaunar in mutu. Ina kuka ne saboda a halin yanzu lokacin da nake shirin ƙaura daga nan duniya ban sani ba ko Allah Ta'ala Yana farin ciki da ni ko kuma a'a.'

              Daga nan sai ya yi addu'a:

'Ya Allah! Wannan shi ne lokaci na ƙarshe a rayuwata (ta duniya). Ka san cewa a ko da yaushe ina ƙaunarka. Don haka ka albarkaci saduwa ta da kai.'


Ya Allah muma ka albarkaci saduwar mu da kai Kasa aljannar Firdausi itace mskomarmu.


*✍️Ahmad Musa

TATTAUNAWAR HUZAIFA (R.A) DA MANZON ALLAH (S.A.Ws) GAMEDA FITINTUNU DA ZASU AUKU KASHI ƊAYA

*Ahmad Musa*

Huzaifa (R.A) yana ɗaya daga cikin Sahabban da suka yi suna. Ana yi masa laƙabi da 'Mai Sanin Asiri.' Manzon Allah (S.A.Ws) ya bayyana masa dukkan sunayen munafukai, sa'annan ya shaida masa irin dukkan fitinun da za su samu Musulmi a jere tun daga lokacin har zuwa tashin ƙiyama.


Ya bayyana masa cikakken (sunan mai tada fitinar, iyayensa da kuma wurin da ya fito da sauransu) da irin abin da zai faru wanda zai shafi kusan mutane ɗari uku ko fiye da haka. Huzaifa (R.A) yana mai cewa: 'Duk sauran mutane, Kowa yakan tambayi Manzon Allah (S.A.Ws) kyawawan abubuwa, amma ni nakan yi masa tambayoyi akan abubuwa marasa kyau, yadda zan iya kare kaina daga gare su.'


Daga nan sai ya ambaci irin abin da ya gudana tsakaninsu da Manzon Allah (S.A.Ws)


Huzaifah:  'Ya Rasulallah! shin za mu koma ga sharri bayan abubuwan da ka zo mana da shi na alheri?'


Annabi:  'Ih, wani sharrin na zuwa.'


Huzaifah:  'Za mu sake samun wani alherin bayan wannan sharri?'


Annabi:  'Huzaifah! Maza tafi ka yi ta karanta Alƙur'ani, kana tunani akan ma'anarsa, sa'annan ka bi dokokin da ke cikinsa.


Wannan abu ya sa Huzaifah ya ƙara nuna damuwarsa ƙwarai da gaske, don haka sai yaci gaba da irin tambayoyi na irin bala'in da za su aukumma Musulmi.


A dakace mu zamu cigaba da bayani akan tambayoyi daya masa gameda fitintunu dazasu auku akashi na biyu insha Allahu.


Muna rokon Allah Maɗaukakin sarki ya datar damu dukkan alkhairi ya kuma kare daga dukkan sharri.


https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1