Monday, September 21, 2020
LABARI TARIHIN MASARAUTAR ZAZZAU
Wannan wata makala ce da muka yi bayan da muka bukaci ku aiko tambayoyinku a kan
tarihin masarautar Zazzau. BBC ta kwashe lokaci mai tsawo wajen bin diddigin
amsoshin tambayoyin naku daga masana tarihin wannan masarauta ta Zazzau. Ita dai
masarautar Zazzau tana daya daga cikin muhimman masarautun kasar Hausa da ma
yankin Afirka ta yamma. Tarihi irin na kunne ya girmi kaka ya yi nuni cewa,
Zazzau wata dadaddiyar masarauta ce, wadda ta samo asali tun daruruwan shekaru
da suka gabata, wato daga lokacin jahiliyya ko kuma kafin zuwan addinin
musulunci. Zazzau Emirate Yadda kalmar ‘Zazzau’ ta samo asali Tushen wannan
kalma ta ‘Zazzau’ yana da rassa biyu, na farko yana da nasaba da yanayin kasar
ta Zazzau, wanda daga Katsinanci ke nufin ‘zo-zo’, wato kasa mai laka, ba mai
rairayi ba, wadda za a iya yin shuka a kanta, kuma ta tsiro. A wani kaulin kuma
‘Zazzau’ na nufin wani takobi, wanda ja-goran jama’a yakan dauka ya jagoranci
jama’a a wajen yaki. Mai daukar wannan takobi ba sarki ake kiransa ba, a wancan
lokaci ana kiran sa ne ‘Madau-Zazzau’, wato ‘Mai Dauke da Zazzau’. Asalin Kalmar
Zariya Zariya kalma ce da ta samo asali daga sunan Zariya ‘yar Sarki Bakwa
Turunku, wadda kanwa ce ga Sarauniya Amina Bambancin Zazzau da Zariya Zazzau
masarauta ce, wadda ta kunshi dukkan kasashe da garuruwan da ke bin masarautar.
Zariya kuwa shi ne babban birnin da sarki yake zaune da hakimai da ’yan
majalisarsa ana gudanar da mulki. Sauran hakimai da suke da kasashe suna kawo wa
sarki rahoto, su kuma ana aika masu da umarni. Kafuwar Masarautar Zazzau Mahaya
dawakin Zazzau A zamanin maguzanci, wato shekaru aru-aru da suka gabata, babu
wani addini da ya shigo, sai al’adu ko rayuwa irin ta maguzanci. Kuma kaura daga
wannan waje, a koma wancan waje, ita ce al’adar Bil’Adama, a kokarin a kokarin
neman wajen da zai zauna ya sami ingatacciyar rayuwa. Mafi yawan ayyukan da
jama’a kan yi a lokacin su ne, noma da kiwo. Wannan lokaci ne kuma masana tarihi
ke kira zamanin ‘Zo-zo’, wato zamanin maguzanci, wanda ya kasance tun kafin
shigowar addinin musulunci. Lokacin da al’umma suka rika taruwa, suna samun
shugabanci, har sarakunan Habe suka fara mulki, aka samu kafuwar Hausa Bakwai,
wato zuri’ar Bayajidda da Sarauniya Daurama. Kuma Zazzau na daya daga cikin
kasashen da aka ba ’ya’yan Bayajida mulki. Bayanin da aka samo daga bakin
Marigayi Malam Habibu Na-Turunku, wani uban gari na Turunku, ya nuna cewa,
Gunguma shi ne sarkin Zazzau na farko, kuma ya yi tafiyayya ne daga Daura, ya bi
ta Kano da Rano, kuma ya fara yada zango a Kangi. Wadanda suka biyo bayansa sun
kafa biranen mulkinsu ne a Kawari da Rikocci da Wuciciri da kuma Turunku, kafin
su je Zariya. Nohir ta auri wani bako, ta haifa masa da namiji, kuma aka sa wa
dan suna dan Bakwa Turunku. Daga baya sunansa ya koma Bakwa Turunku, wanda ya
gaji sarautar kawunsa Kawanissa a shekarar 1536. Bakwa Turunku ya yi sarauta ne
a garin Turunku, kuma har yanzu akwai sauran kufan masarautar ta Turunku a can
kasan tsaunukan da suke shimfide a yankin gabashin Zariya. Kafuwar birnin Zariya
Kamar yadda aka sami labari daga wajen Marigayi Malam Habibu Na-Turunku, wani
uban gari na Turunku, ya nuna cewa, Zariya ‘yar Bakwa Turunku, kuma kanwar
Sarauniya Amina ce ta kafa birnin Zariya, don haka ake kiran birnin da sunanta.
Hakan kuwa ya biyo bayan yadda hedikwatar mulki ta Zazzau ta yi ta sauya wuri
saboda matsalar rashin ruwa, a zamanin mulkin Bakwa Turunku, wato mahaifin
Sarauniya Amina da Zariya. Hedikwatar ta tashi daga Bomo zuwa Wucicciri zuwa
Ancau zuwa Kargi, ta koma Turunku. A wancan lokaci an ce sai Bakwa ya ga Turunku
ta yi wa mutanensa kadan a matsayin hedikwatar mulki, ga matsalar ruwa ana fama
da ita. Saboda haka, sai ya koma Zariya a shekarar 1537. Daga nan ne kuma
masarautar Zazzau ta koma Zariya. Amma ba a shiga Zariya kai tsaye ba, sai Bakwa
Turunku ya gaya wa ‘yarsa Zariya, cewa ta je wajen kufannin iyayensu, wato
Kufena kenan, ta je ta fara zama a wurin, kuma akwai rafi a wajen. Sai dai da
Sarauniya Amina, wadda ita ce 'ya a wajen Zariya, ta dawo daga yake-yakenta, sai
ta ce wurin ya yi fadi da yawa. Idan aka gina hedikwatar mulki a wurin a wancan
zamani na yake-yake, to mahara za su iya kai masu hari. Saboda haka, ta ce a
koma kusa da rafin da ake kira Fadamar Bono a cikin gari, wanda daga baya da
Fulani suka karbi mulki suka mayar da sunan zuwa Fadamar Sarki. Da aka gama sake
shata gari, sai Sarauniya Amina ta sa wa wannan zagayen da’irar da aka yi sunan
kanwarta, wato Zariya. Don ta girmama suna ‘yar uwarta, kuma dalilin sunan garin
Zariya kenan. Kuma ta gina gida a cikin gari, inda ya zama fadar Zazzau, inda
mahaifinta ya zauna, kuma har yanzu nan ne fadar masarautar Zazzau. Ana kiran
gidan da sunan ‘Gidan Bakwa’. Asalin Ganuwar Zazzau A zamanin da, mai karfi shi
ke da iko a kasashen Hausa da sauran wurare, saboda haka kowacce kungiyar
al’umma da suke so su yi karfi, sai sun kewaye kansu, yadda mahara ba za su
shigo masu ba. Wannan shi ne dalilin ganuwa a kasar Hausa, kuma inda duk aka yi
ta, an yi ne don wurin ya zama hedikwatar mulki na al’ummar wajen. To, a Zazzau
wadanda suka fara yin ganuwa a cikin gari, aka mayar da cikin gari hedikwata,
wato babban birnin mulki na Zazzau, su Bako Turunku ne, mahaifin Sarauniya Amina
ta Zariya. Ganuwar Zariya, ita ce ta dauka tun daga dutsen Kufena, ta kewaya
zuwa Hanwa, ta shigo wajen barikin soja, inda ake kira Jushin Waje. Ta biyo ta
Kofar Galadima, ta Kofar Kona, ta hada da rafin Saye, sannan ta koma ta
Gwargwaje, ta hadu da Wusasa, kana ta koma Kufena. Saboda sanin dabarun yaki,
sai Sarauniya ta sa bawanta, wato Bono, ya je ya sara da’ira da rafin Sarki a
tsakiya ya kewaya aka yi kofofin garin guda takwas, wadanda suka hada da Kofar
Kibo, da Kofar Kona da Kofar Galadima, da Kofar Bai, da Kofar Doka wadda a da
ake kira Kofar Kano, da Kofar Jatau, da Kofar Kuyambana da kuma Kofar Gayan.
Sarauniya Amina Sarauniya Amina Habe ce ta Zazzau, sai dai wasu masana tarihi na
kallon ta a matsayin Sarauniya, amma ba Sarki ba ce, don haka babu sunanta a
jerin sarakunan Habe. Ma’ana, akwai sarautu da ake ba ’ya’ya mata a da a
karkashin sarautar Habe. Alal misali, akwai Sarauniya, akwai Gimbiya, akwai Iya,
akwai Madanni, da dai sauran su. Duk wadannan sarautu ne na ’ya’yan sarakunan
Habe. Saboda haka, Sarauniya Amina ba wai ta zama ita ce Sarki ba, a lokacin
mahaifinta (Bakwa Turunku) yana sarki, ita kuma tana matsayin sarauniya, wato
babbar ’yar sarki. Bisa al’ada, babban dan sarki shi ne shugaban rundunar sojoji
na wannan masarauta. To, ita Amina ita ke rike da wannan kambi, kuma ita ta yi
ta yake-yake. Ta buga daga Zazzau ta yi arewa har Kano, har Katsina, ta kare
iyakokin masarautar Zazzau. Ta yi kudu da yamma, don kara fadi kasa da karfin
mulki, kuma da haka ne ta dangana da kasar Naija ta yanzu, ta dangana da kasar
Idah, wato kasar Attah Gara a jihar Kogi. Ta je har kasar Nasarawa ta yau,
saboda karfin yaki da iya gudanar da yaki da jaruntaka. Tana da rundunoni da
take jagoranta, kuma duk inda suka tunkara suna yin nasara, kamar yadda tarihi
ya nuna. QUEEN AMINA Sarakunan Habe Tarihi ya nuna cewa, an yi sarakuna sittin
na Habe, wadanda suka mulki masarautar Zazzau tun daga kan Gunguma, wanda shi ne
ya fara yin sarauta a matsayin ‘Madau-Zazzau’ na farko a wancan lokaci, kuma shi
jika ne na Bayajidda. Habe sun kwashe shekaru fiye da dari suna mulki, har ya
zuwa lokacin mulkin Sarkin Zazzau Makau, wanda shi ne na karshe a jerin
sarakunan na Habe, wanda shi ne ya fara zuwa Suleja (wadda aka fi sani da Abu-Ja
tun asali). Ga kuma jerin sunayen sarakunan na Habe: Gunguma Matazu Tumsah
Tumusa Suleman Maswaza Dinzaki Nagogo Katchina Nawanci Macikai Kawo Bashi Kar
Majidadi Dihirahi Jinjiku Sakannu Monan Abu daga shekarar 1550 zuwa 1530 Gidan
Dan Masukanan daga shekarar 1530 zuwa 1532 Nohir daga shekarar 1532 zuwa 1535
Kawanissa daga shekarar 1535 zuwa 1536 Bakwa Turunku daga shekarar 1536 zuwa
1539 Ibrahim daga shekarar 1539 zuwa 1566 Karama daga shekarar 1566 zuwa 1576
Kafo daga shekarar 1576 zuwa 1578 Bako daga shekarar 1578 zuwa 1581 Aleyu I daga
shekarar 1581 zuwa 1587 Isma’ilu daga shekarar 1587 zuwa 1598 Musa shekarar 1598
Gadi daga 1958 zuwa 1601 Hamza shekarar 1601 Abdullah daga shekarar 1601 zuwa
1610 Burema daga shekarar 1610 zuwa 1613 Aleyu II daga shekarar 1613 zuwa 1640
Muhammad Rabo daga shekarar 1640 zuwa 1641 Ibrahim Basuki daga shekarar 1641
zuwa 1654 Bako II daga shekarar 1654 zuwa 1657 Sukana daga shekarar 1657 zuwa
1658 Aeyu III daga 1658 zuwa 1665 Ibrahim daga shekarar 1665 zuwa 1668 Muhammad
Abu daga shekarar 1668 zuwa 1686 Sayo Ali daga shekarar 1686 zuwa 1696 Bako Dan
Musa daga 1696 zuwa 1701 Is’haq daga shekarar 1701 zuwa 1703 Burema Ashakuka
1703 zuwa 1704 Bako Dan Sunkuru daga shekarar 1704 zuwa 1715 Muhammad Dan
Gunguma daga shekarar 1715 zuwa 1726 Uban Bawa daga 1726 zuwa 1733 Muhammad Gani
daga shekarar 1733 zuwa 1734 Abu Muhammad Gani shekarar 1734 Dan Ashakuku daga
shekarar 1734 zuwa 1737 Muhammad Abu daga shekarar 1737 zuwa 1757 Bawo daga
shekarar 1757 zuwa 1759 Yunusa daga shekarar 1759 zuwa 1764 Yakubu daga shekarar
1764 zuwa 1767 Aleyu IV daga shekarar 1767 zuwa 1773 Cikoku daga shekarar 1773
zuwa 1779 Muhammad Maigamo daga shekarar 1779 zuwa 1782 Is’haq Jatau daga
shekarar 1782 zuwa 1802 Muhammad Makau daga shekarar 1802 zuwa 1804 Yadda wasu
wurare suka fita daga masarautar Zazzau Lokacin da Shehu Usman Danfodiyo ya kawo
jihadi a wuraren Hausa Bakwai da Banza Bakwai, Malam Musa yana jagorancin yaki.
A tarihince, an ji cewa an kama Zazzau ba tare da an kashe ko da mutum daya ba.
Malam Musa ya shiga Zazzau ta Kofar Bai, a lokacin sarkin Zazzau na karshe na
Habe, Sarki Makau ya fita da dakarunsa, ya bi hanyar Hunkuyi, hanyar Kudan,
hanyar Kano, tun da an ba shi labari cewa, Malam Musa zai biyo ta hanyar Kano,
to sai ya bi wannan hanya. Shi kuma Shehu Usman Danfodiyo, sai ya ba Malam Musa
shawara to ya kauce wa wannan hanya. Ana ganin hakan ba ya rasa nasaba da irin
ilhamar manyan malamai na da, bayin Allah, suna addu’a, suna rokon Allah Ya ba
su haske da ilhamar yadda abubuwa za su kasance. Sai aka fada wa Malam Musa,
cewa kar ya bi waccan hanya ta Kano, ya zagaya ya bi ta garin Likoro. Kuma haka
ya bi, ya zagaya ya bi Farin Kasa da ke kasar Soba ta yanzu, sannan ya bullo wa
Zariya ta Kofar Bai, ya kuma shiga garin. Bayan shi kuwa Sarki Makau yana ta
baryar arewa maso gabas, yayin da Malam Musa ya bullo ta arewa maso yamma,
saboda haka ba a hadu an gwabza yaki ba. Da haka Malam Musa suka shiga cikin
birnin Zariya, suka rufe kofofin birnin, Sarki Makau na waje, yana jira, sai
labari ya isa gare shi, cewa ai Fulani sun shiga Zariya sun kulle kofofi, wato
an kori su Sarki Makau kenan. Daga can Sarki Makau ya gudu, ya nufi kudanci, ya
je nan, ya je can, don a lokacin akwai sarakuna irin su Sarkin Fatika da Sarkin
Kajuru da Sarkin Kauru da sauran su, wadanda duka da suna bin Sarkin Zazzau na
Habe. Amma da Fulani suka zo, sai suka yi wa Sarki Zazzau Makau tawaye, suka bi
Fulani. Suka ci gaba da biyayya, suka kuma zauna a karkashin Sarkin Zazzau
musulmi, Bafulatani. Da haka fadin kasar Zazzau ya fara raguwa. Bayan da Sarki
Makau ya bar Zazzau, ya nufi kudanci yana neman goyon bayan kananan sarakunasa
da ke can gefe, wadanda tun zamanin Sarauniya Amina aka ci su da yaki, suna
biyayya ga masarautar Zazau. To, Shehu Usman Danfodiyo ya ce, idan mayakan Malam
Musa sun sadu da wani wuri da wani babban dutse a kudu maso yamma da Zazzau, su
tsaya a wurin. Iyakar daular da yake so ya tabbatar kenan. Inda Makau ya tafi,
ya wuce wannan wuri, to, kar su bi shi. Hakan ne kuma aka yi. Wannan shi ya sa
aka kafa Zazzau Suleja a wurin, shi Sarkin Zazzau Makau shi ya tsaya a nan, kuma
dakarun Malam Musa ba su ci gaba da bin su ba, suka koma Zariya. Saboda haka, ba
a yi yaki da ya wuce wannan wuri ba. Wato dai masarautar Suleja daga Zazzau ta
fito, don haka har gobe masu sarautar Suleja suke kiran kansu da mukamin Sarkin
Zazzau, amma Suleja. Shi ya sa za ka ji ana cewa, Sarkin Zazzau Suleja. Kuma duk
sunayen unguwannin da ke cikin birnin Zariya, su ne za ka samu a Suleja, kamar
su Kwarbai, Anguwan Fatika, su Kusfa, Anguwan Iya da dai sauransu. Saboda sun
maimaita wadannan abubuwa da suka baro a Zariya. Sai dai kuma a wani kaulin, an
ce Malam Musa ya ziyarci Zariya ne tun kafin jihadin Shehu Usumanu Danfodiyo,
kuma ya zauna a birnin yana koyar da karatun Al-Kur’ani da sauran littattafan
addinin musulunci. To, da jihadin ya shigo, ya kasance yana cikin mukarraban
Mujaddadi Shehu Usumanu Danfodiyo, kuma ya sami matsayin ja-goran yaki. Da haka
Malam Misa da mayakansa suka kai hari ga Muhammadu Makau, Sarki na sittin a
jerin sarakunan Habe, a ranar Asabar goma ga watan Zulhaji a shekarar 1804,
lokacin yana filin sallar Idi da ke wajen garin Zariya. Duk da yake dai
Muhammadu Makau yana tare da dimbin mazaje tare da shi a lokacin harin, an ci
shi da yaki. Saboda ba sa iya komawa cikin gari su dauko makamansu. Don haka aka
tilasta masa tserewa tare da wasu magoya bayansa zuwa Zuba da ke kudancin yankin
masarautar Zazzau, inda a can ne ya yi tirjiya ga hare-haren Fulani. Daga cikin
mutum dubu uku da ke tare da shi akwai ‘yan uwansa Abu-Ja da Abu-Kwaka. A wannan
wuri ne Sarki Makau ya zauna, kuma wadanda suka gaje shi suka karfafa, suka kafa
wata sabuwar masarautar Zazzau ta Habe mai cin gashin kanta a kasar da daga baya
aka rika kira Abuja. Da ma kuma jama’ar yankin suna biyayya ga sarakunan Zazzau.
Wannan masarauta ta Habe ta rayu har ya zuwa lokacin zuwan Turawan mulkin
mallaka na Birtaniya, duk kuwa da matsanantan hare-hare da Fulani ke kai masu.
Kuma sarakunann Zazzau na Abuja, sun rike mukaman da suke da su na asali tun
daga Zariya. Sarakunan Habe na Suleja (Abu-Ja) Sarakunan Habe na Suleja (Abuja),
sun samo asali ne daga tsatson Is’haq Jatau, Sarkin Zazzau na hamsin da tara a
Zariya, wanda ya yi sarauta daga shekarar 1782 zuwa 1802. Ga kuma jerin
sarakunan da suka yi mulki a wannan masarauta ta Suleja (Abu-Ja) daga farko zuwa
yau: Muahammadu Makau daga shekarar 1804 zuwa 1825 Abu-Ja daga shekarar 1825
zuwa 1851 Abu-Kwaka daga shekarar 1851 zuwa 1877 Ibrahim Iyalai daga shekarar
1877 zuwa 1902 Muhammad Ganu daga shekarar 1902 zuwa 1917 Musa Angulu daga
shekarar 1917 zuwa 1944 Suleman Barau daga shekarar 1944 zuwa 1979 Ibrahim Dodo
Musa daga shekarar 1979 zuwa 1993 Muhammad Awwal Ibrahim daga shekarar 1993 zuwa
yanzu A yanzu dai akwai masarautu biyu na Zazzau, wato Zazzau ta Fulani da ke da
hedikwata a Zariya, da kuma Zazzau ta Habe mai hedikwata a Abuja wato wurin da a
yanzu aka fi sani da Sule-Ja). Sarakunan Fulani A lokacin da Shehu Usmanu
Dafodiyo ya yi jihadi daga shekarar 1804, kasar Zazzau ta dangana da inda Habe
suka tsaya, wato kasar Idah a jihar Kogi ta yau. A zamanin Sarkin Zazzau, Malam
AbdulKarim, daga baryar kudu masarautar Zazzau ta dangana da har zuwa inda a
yanzu ake kira Nasarawa, kuma har zuwa gabar kogin Benuwai. A baryar arewa kuwa
ta yi iyaka da sauran kasashen Hausa bakwai, kamar Katsina ta fuskar arewa, da
Kano ta fuskar arewa maso gabas, sai Bauchi da Filato a arewa maso yamma. Kuma
daga Zazzau ne ake nada sarakunan kasashen da ke karkashin masarautar ta Zazzau
Sarkin Zazzau na farko a karkashin daular Usumaniyya, shi ne Malam Musa, wanda
Shehu Usumanu Danfodiyo ya ba tutar jaddada musulunci a kasar Zazzau, kuma na
karshe kuma shi ne Sarkin Zazzau Makau wanda Turawan mulkin mallaka suka kawar.
Ga kuma jerin sunayen sarakunan Zazzau na Fulani: Malam Musa daga shekarar 1804
zuwa 1821 Malam Yamusa deaga shekarar 1821 zuwa 1834 Malaam AbdulKarimu daga
shekarar 1834 zuwa 1846 Malam Hammada daga shekarar 1846 zuwa 1853 Mamman Sani
daga shekarar 1846 -1853 Sidi AbdulKadir daga shekarar 1853-1853 Malam
AbdusSalami daga shekarar 1853 zuwa 1854 Malam AbdulLahi (nadi na farko) daga
shekarar 1857 zuwa 1871 da (nadi na biyu) daga shekarar 1874 zuwa 1879 Malam
Abubakar daga shekarar 1879 zuwa 1888 Muhammadu Sambo daga shekarar 1888 zuwa
1890 Muhammadu Yero daga 1890 zuwa 1897 Sarki Malam Kwasau daga 1897 zuwa 1902
(shi ne sarki na karshe kafin zuwan Turawa) Zuwan Turawan mulkin mallaka Alu Dan
Sidi (shi ne Sarkin Zazzau wanda Turawan mulkin mallaka suka fara nadawa) daga
shekarar 1903 zuwa 1920 Sarki Dalhatu daga shekarar 1920 zuwa 1924 Sarki Ibrahim
Dan Sarkin Zazzau Kwasau daga shekarar 1924 zuwa 19337 Sarki Jafaru daga
shekarar 1937 zuwa 1959 Alhaji Muhammadu Aminu daga shekarar 1959 zuwa 1975
Alhaji Shehu Idris (wanda ke kan karagar mulki yanzu) daga shekarar 1975 zuwa
yau Gidajen Sarautar Zazzau A karkashin Daular Fulani, masarautar Zazzau tana da
gidaje hudu, wadanda suka hada da: · Gidan Mallawa, wanda Malam Musa ya kafa, 1.
Sarkin Zazzau Malam musa 2. Sarkin Zazzau Malam Abdulkadir dan Musa 3. Sarkin
Zazzau Malam Abubakar dan Musa 4. Sarkin Zazzau Malam Alu Dan Sidi. · Gidan
Barebari, wanda Yamusa ya kafa, 1.Sarkin Zazzau Malam Yamusa 2. Sarkin Zazzau
Malam Hammada dan Yamusa 3. Sarkin Zazzau Malam Mamman Sani dan Yamusa 4. Sarkin
Zazzau Malam Abdullahi dan Hammada 5. Sarkin Zazzau Malam Yero dan Abdullahi 6.
Sarkin Zazzau Malam Kwasau dan Abdullahi 7. Sarkin Zazzau Malam Dalhatu dan Yaro
8. Sarkin Zazzau Malam Ibrahim dan Kwasau 9. Sarkin Zazzau Malam Ja'afaru dan
Isiyaku · Gidan Katsinawa, wanda Malam AbdulKarim ya kafa, 1. Sarkin Zazzau
Malam Abdulkarim 2. Sarkin Zazzau Malam Sambo dan Abdulkarimu 3. Sarkin Zazzau
Malam Muhammadu Aminu 4. Sarkin Zazzau Malam Shehu dan Idrisu Auta · Gidan
Sullubawa (Fulani), wanda Malam AbdusSalam ya kafa. 1. Sarkin Zazzau Malam
Abdulsalam Kowanne gida dai ya biyo asalin inda wanda ya kafa shi ne ya fito.
Mallawa Fulanin Futo Toro ne da suka fito daga kasar Mali, Barebari kuma sun
fito ne daga Kukawa a yankin da a yau aka fi sani da Jihohin Barno da Yobe, amma
asali su Fulani ne, kuma ana kallon su ne a matsayin Fulani. Saboda haka ne ma
ake kiransu da Fulata-Barno. Haka Sullubawa Fulani ne da suka fito daga yankin
jihohin Sakkwato da Kebbi, kuma yadda AbdusSalami Basullube ya sami sarautar
Zazzau kenan. Yadda aka sami gidaje hudu na sarautar Zazzau Gidan sarautar
Zazzau ya kasu hudu ne, saboda Zazzau kasa ce wadda ta tattara dimbin al’umma da
suka fito daga wurare daban-daban, don neman ilimin addinin musulunci. Saboda
haka, a lokacin da jihadin Shehu Usman Danfodiyo ya zo, an sami malama ne masana
ilimin addinin musulunci, da shari’o’i, da kuma ka’idar mulki na musulunci. A
lokaci ba wai ana la’akari ne da cewa wane ya gada ko wane ne ya gada ba, ana
neman wanda zai zama khalifa, don tabbatar da kafuwar addinin musulunci a
Zazzau. Zazzau wata cibiya ce, tun ma kafin jihadi Shehu Usman Danfodiyo, saboda
kasancewarta ‘Zo-zo’, kasa mai albarka, mai daukar komai da komai na noma, tana
da laima da ni’ima. Kowa yana son ya je ya zauna a Zazzau, ya amfana ta fuskar
noma da kiwo. Wannan ya sa Fulani da yawa suka zauna a Zazzau tun zamanin mulkin
Habe, kuma da yawansu abin da suke yi baya ga kiwo, shi ne karatun addini. Kuma
lokacin da dan uwansu Shehu Usman Danfodiyo ya bullo, sun kai masa gaisuwar
caffa, suka yi masa mubayi’a, ya yarda da su. Suka zauna da shi, suka yi karatu
tare da shi, suka yi yake-yaken da aka yi tsakanin Sarkin Gobir da Usman
Danfodiyo. Tun kafin a yi ganuwa, akwai mutane, wato Fulani, irin su Malam Musa
da Yamusa da Malam AbdulKarim da su AbdulSalam da ke zaune a cikin garin Zariya,
suna koyarwa ta addinin musulunci. Da suka ji bullowar Shehu Usman Danfodiyo
yana zuwa wurare daban-daban yana kira da a gyara addinin musulunci, suka yadda
da abin da yake yi, suka yi masa mubaya’a Tarihi ma ya nuna cewa, Malam
AbdulKarim ya zauna da Shehu Usman Dan Fodiyo, ya yi karatu a wajensa. Shi kuwa
Malam Musa kusan tsaran Shehu Mujaddadi ne, kuma tare suke tafiye-tafiye. Gidan
Malam Musa Malam Musa shi aka ba tutar sarauta a lokacin da jihadi ya iso
Zariya, Malam Musa shi aka ba wannan tuta, don ya yi jagoranci, kuma bayan
mutuwar Malam Musa, ba a mayar da sarautar ta zama gado ba. To, bayan mutuwarsa
ba a mayar da abin ya zama gado ba, sai aka ba wani daga cikin malaman da suke
tare da Shehu Usman Danfodiyo, wato Malam Musa. Kuma Shehun ne da kansa ya ba
shi tutar halifanci. Gidan Malam Yamusa Kana sai Shehu Usman Danfodiyo ya ba
Malam Yamusa shugaban rundunar sojojin yaki na Malam Musa a matsayin Madakin
Zazzau. Gidan Malam AbdulKarimu Shi kuma Malam AbdulKarimu, Shehun ya ba shi
sarautar Sa’in Zazzau, wato mai ilimin rabon arzikin kasa.Ya san masu dabbobi da
suka cancanci bayar da zakka, ya san manoman da suka cancanci bayar da zakka, ya
san nisabin dukiyar da za a fitar wa zakka. Ya kuma san su wa ya kamata a ba
zakkar. Gidan Malam AbdulSalam Shi kuwa Malam AbdulSalami yana cikin dalibai
Fulani wadanda suka yi amfani wajen taimakon Shehu Usman Danfodiyo a yake-yaken
da ya yi tsakaninsa da Sarkin Gobir. Amma shi ba ya bullo ne kamar yadda su
Malam Musa da Yamusa da AbdulKarimu suka bullo ba. Hawan Malam AbdulSalam kan
gadon sarauta ya kasance raba-gardama ne, saboda lokacin da sarautar Zazzau ta
koma gado, ’ya’yan gidan sarakunan guda uku suka fara cewa sai daga cikinsu ne
za a sami wanda zai zama sarki a Zazzau, sai ‘ya’yan Sarkin Zazzau Yamusa suka
fara irin wannan sarautar. Inda Hammada ya fara sarauta, daga nan sai kanensa
Mamman Sani. Bayan Mamman Sani ya kau, sai Sidi AbdulKadir, babban dan Malam
Musa da Shehu Usman Danfodiyo ya ba tuta, ya zama sarki bisa gado. Shi ma yana
da ilimin addini, kuma ya cancanci rike sarautar. Sai dai bayan da Sidi
AbdulKadir ya zama sarkin Zazzau, an yi ta samun kwamacala da rigingimu, tun da
abin ya zama gado kowa ma dan gida yana ganin ya cancanci rike sarautar. Daga
nan aka fara samun rashin yarda da juna, har aka kai kara Sakkwato, aka dakatar
da Sarkin Zazzau Sidi AbdulKadir daga sarauta. Shi kuma ya ce, duk zargin da ake
masa na sarautar ba shi kadai yake sarautar ba. Tare da shawarar dukkan ’yan
majalisarsa ake yi, wato su masu son a ba su sarautar nan. Saboda haka, ba wanda
ya cancanta a cikinsu, kamar yadda shi ma bai cancanta ba. Saboda haka, sai
sarkin musulmi na wancan lokaci ya ga ya fi dacewa a dauko wani malami cikin
daliban Shehu Danfodiyo a ba shi jagoranci, duk da ya manyanta a wannan lokaci.
Kuma lokacin ya yi tsawo, Malam Musa ya yi shekaru goma sha, Yamusa ya yi
shekaru goma sha, AbdulKarim ya yi shekaru goma sha, Hammada ya yi ’yan kwanaki,
Mamman Sani ya yi shekaru, Sidi AbdulKadir ya yi wata takwas zuwa goma a gadon
sarauta. To, idan ka tara wadannan shekaru, ka ga an dumfari shekaru arba’in.
To, shi Malam AbdulSalam idan ka dora shekara arba’in a kan shekarunsa, ka ga ya
manyanta. Amma sai sarkin musulmi na wancan lokaci ya ce a ba AbdulSalami
sarautar Zazzau ya rike. Da haka ya zama raba-gardama. Ba a ba kowa ba daga
cikin ‘ya’yan wadancan sarakuna. Wannan kuma shi ne dalilin zuwan gida na hudu a
sarautar Zazzau kenan, wato don a sami natsuwa. Ta haka ne aka sami wadannan
khalifofi guda hudu, kuma kowannensu an ba shi sarauta ne a matsayin kansa na
masanin addinin musulunci, na mai biyayya da gaskata abin da jihadin Shehu Usman
Danfodiyo ya kawo bisa koyarwa Alkur’ani da Sunnar Manzon Allah (SAW). Tarihin
Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris Haihuwa da Tsatson Sarki Mai
martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris, an haife shi ne a watan Maris
na shekarar 1936. Wanda ya haife shi ne Mai Unguwa Auta. Sunan na Auta aka fi
sani, amma sunansa na Littafi shi ne Idrisu. Shi da ne, dan autan Mai Martaba
Sarkin Zazzau Muhammadu Sambo. Shi kuma Sarki Muhamadu Sambo da ne, kuma na biyu
a cikin ‘ya’yan Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim. Shi kuma Sarkin Zazzau Malam
AbdulKarim shi ne na farko a daular Fulani karkashin jaddada addinin musulunci
da Shehu Usumanu Danfodiyo ya yi a kasar Zazzau, kuma shi ne ya assasa gidan
Katsinawa a sarautar Zazzau. Ina Sarki ya taso? Shi Mai martaba Sarki lokacin
mahaifinsu yana Mai Unguwa a unguwar Iya a nan aka haife shi. Unguwar Iya wata
unguwa ce da ke tsakanin unguwar Durumi da Kuyanbana. A nan ya girma, ya shekara
akalla bakwai, inda har ya shiga makarantar allo, ya fara karatun addini. A nan
dai unguwar Iya ya yi makarantar farko da Bature ya gina a cikin birnin Zariya,
wadda ake kira ‘Town School one’, ita ce kuma makaranatar ‘Kofar Kuyanbana Local
Government Education Primary School’. Yanzu ana ce mata ‘Waziri Lawal Local
Government Education Primary School’, a nan ya fara karatu. Bayan ya gama sai ya
tafi Alhudahuda College, lokacin ana kiran makarantar da sunan ‘Middle School’.
Daga nan aka yi masa sauyi, ya koma makarantar koyar da malunta a Katsina
lokacin ana kiran ta ‘Katsina Teachers’ College’.To, a nan ya koyi aikin
koyarwa, wanda shi ne babbar sana’arsa ta farko da ya iya. Daga baya mai martaba
ya sauya daga malamin makaranta ya shiga aikin mulki, wanda har ya je kasar
Ostireliya (Australia). Yana cikin daliban farko da ofishin jakadancin
Ostireliya suka dauki dawainiyarsu suka je suka yi karatu na koyon ilimin mulki
a kasar ta Osireliya Wuraren da ya yi aiki Daga shekarar 1956 ya koyar a wurare
daban-daban a cikin garin Zariya da kauyuka. Ya koyar a Zangon Aya, ya koyar a
Paki, har ya yi hedimasta a Pakin. Ya kuma yi hedimasta a Hancin Kare a
makarantar ‘Town School No.3’’. A shekarar 1962 ya koma aikin mulki, lokacin da
ya koma karkashin hukumar ‘NA’ (Native Authority) ta Zariya a zamanin Sarkin
Zazzau Aminu. Inda ya gwama aiki biyu, wato yana aiki a hukumar ‘NA’, kuma yana
aiki a matsayin jami’in sadarwa na hukumar kula da kananan hukumomi da masarautu
na jihar Arewa. Daga baya Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu ya ba shi
mukamin Babban sarakatare na musamman na sarki. Daga nan ne sai aka nada shi
sarauta, ya zama wakilin ofis, wato mai daukar nauyin duk abin da ya shafi aikin
masarauta a karkashin ‘Native Authority’ a wannan lokacin. Ya rike wannan mukami
na tsawon kamar shekara biyu zuwa uku, sai Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu
Aminu ya nada shi hakimin birni da kewaye, mukamin da ya rike na tsawon shekara
biyu zuwa uku, yana hakimi. Kuma Dan Madamin Zazzau. A shekarar 1975 likafarsa
ta yi gaba, aka ba shi a sarautar Sarkin Zazzau. Sauyin da ya kawo a sarautar
Zazzau cikin shekaru arba’in da biyar yana mulki Makusantan Sarkin suna ganin ba
wani al’amari da ya shafi rayuwar Zage-zagi a birnin Zariya ko a masarautar
Zazzau ne da ba a sami ci gaba ba. Ta fuskar ilimi, tun daga kananan makarantun
firamare zuwa sakandire, zuwa na gaba da sakandire, zuwa jami’o’i, makarantun
sojoji da sauransu da aka yi a masarautarsa, akalla ba za a rasa makarantu
ashirin ba. Iyalin Sarki Allah Ya albarkaci mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji
Dokta Shehu Idris da iyali masu yawa. Yana da mata hudu, da ‘ya’ya maza da mata
da yawansu ba zai gaza arba’in da biyu ko da biyar ba. Dabi’u da halayen Sarki
Daya daga cikin hakiman masarautar Zazzau, Salanken Zazzau, Dokta Muhammadu
Bello AbdulKadir, ya ce, babbar baiwar da Allah Ya yi wa mai martaba Sarkin
Zazzau, Alhaji Shehu Idris, shi ne hakuri, yana da hakuri matuka. Ga shi kuma
yana da kawaici, wanda a sakamakon haka ne ya kai kusan shekara ashirin yana
sarauta, amma bai nada kowa daga cikin ‘ya’yansa sarauta ba, saboda kawaici. Sai
da dattawa suka matsa masa, cewa idan bai nada ‘ya’yansa a sarauta ba, wa zai
nada masa su. Hakurinsa da dauriya suka sa Zazzau ta zama kowa ya zo karbabbe
ne, zai zo ya sami karbuwa wajen al’umma ya yi kasuwanci, ko ya nemi ilimi, ko
ya yi kasuwanci ko sana’a da sauransu. Don haka, birnin Zariya ya zama wata
matattarar kowacce kabila daga sassa daban-daban na Najeriya; ba kabilar da ba
za ka samu ba a masarautar Zazzau. Masallacin Juma’ar masarautar Zazzau Zazzau
wurin ne wanda tun kafin bullowar jihadin Shehu Usman Danfodiyo akwai
rukuni-rukuni na Fulani a cikin gari da kauyuka wadanda aikinsu shi ne bayar da
karatu na addinin musulunci. Kuma tun a wannan lokaci akwai masallacin juma’a a
unguwar Juma cikin birnin Zariya, wanda aka gina a zamanin mulkin Isiyaku Jatau
wanda Habe ne. Malaman unguwar Juman nan ko da aka yi jihadi sun ci gaba da
limanci, kuma har yau su ke limanci, tun da su ma Fulani, kuma an same su da
iliminsu. Ko da Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim ya gina masallaci a kofar fada,
wancan masallacin na unguwar Juma ya rushe, an ci gaba da yin sallar Juma’a tare
da limanci wadannan Fulani na unguwar Juma.Har yau zuri’arsu ke limanci. Abin da
kasar Zazzau ta ginu a kai Ita Zazzau kasa ce da ma da ta ginu ne a kan abubuwa
biyu, wato ilimin addinin musulunci, da harkar noma da kiwo. Kuma ko da Shehu
Usman Danfodiyo ya yi jihadinsa abin da ya karfafa kenan. Wasan Kanawa da
Zage-zagi Kamar yadda masana tarihi kan fada, mai karfi shi ke da iko. To, a
wancan zamani, daular da ta yi karfi sai ta yunkura ta je ta mamaye wata. To,
inda aka yi nasara, sai ka ji, amma inda aka gwabza, aka yi kare jini biri, ko
kuma kowa ya tare kan iyakarsa, sai ka ji irin wadannan wasannin suna aukuwa.
Haka ma inda aka sami nasarar cin su da yaki, sai ka ji irin wannan wasa yana
faruwa. Misali za ka ga Katsinawa da Gobirawa ana irin wannan wasa. To, Kanawa
da Zage-zagi ma akwai wannan wasa, cewa ita Sarauniya Amina ta kai hari Kano har
Kofar Mata. Wannan kofar ai ana cewa nan ne aka dakatar da Sarauniya Amina, aka
hana ta shiga cikin birnin Kano. A wancan zamani na mulkin Habe dai, an ce an
wani sarkin Kano ya kawo farmaki har Zariya, amma aka tare shi a tsakanin yankin
da a yanzu aka sani da karamar hukumar Kubau, wajen garin Kargi. Aka yi
ba-ta-kashi. Saboda haka, ba mamaki ka ji ana wasa tsakanin Fulani da Barebari,
tsakanin Katsinawa da Gobirawa, tsakanin har Yarabawa da Gobirawa. Kuma za ka ga
irin wannan wasa yana dada dinke zumunci ne, ba yana batawa ba ne. Wannan dai
duk a zamanin mulkin Habe ne aka yi ire-iren wadannan hare-hare. Amma yayin da
aka sami shigowar daular Usumaniyya, sai kasashen suka zama daya, addinin
musulunci ya hade su. Saboda haka, wata kasa ba ta kai wa wata kasa farmaki ba a
cikin titocin da Shehu Usumanu Danfodiyo ya kafa. Sun zama abokan aiki, abokan
hulda, kuma abokan shawarar juna. Girman kasar masarautar Zazzau a halin yanzu
Sauyin da aka samu bisa sabon tsari na gwamnati, a yanzu a kowacce karamar
hukuma ana da gundumomi ashirin da uku wadanda hakimai suke mulki a karkashin
Mai Martaba Sarkin Zazzau. Kamar dai yadda gwamnatin jiha mai ci yanzu ta mayar
da su. Amma gwamnatin baya ta nunnunka wadannan gundumomi, saboda ana shigo da
harkar siyasa a cikin masarautun. Wata gwamnatin ta zo ta kara gundumomi, har
sun kai tamanin da shida, ita kuma wannan gwamnati da ta zo sai ta rage su zuwa
ashirin da uku. A zamanin mulkin soja an yanke wasu kananan hukumomi da ke
kudancin jihar Kaduna, wadanda ke lardin Zazzau, wadanda suka hada da Kaciya da
Zonkwa. Ta yankin kudu, sai aka bar lardin na Zazzau da kananan hukumomin Igabi
da Kaduna ta kudu da Kaduna ta Arewa. Ta arewa akwai kananan hukumomin Giwa da
Kudan, ta gabas kuwa akwai Makarfi da Ikara da Kubau. A yankin tsakiya kuwa
akwai kananan hukumomin Soba da Sabon Gari da Zariya. A yanzu kananan hukumomi
goma sha daya da gundumomi ashirin da uku kenan suke bin masarautar Zazzau a
yau. A da kuwa tun daga karamar hukumar Kaciya, zuwa Chikun, har zuwa Kagarko,
duk suna bin Zazzau ne. Amma daga baya aka sami wata gwamnati ta soja ta yanke
wadannan kananan hukumomi, ta yi wasu sababbin masarautu, abin da ya sa aka sami
masarautu kusan talatin da biyu. Saboda ra’ayin siyasa na son a ba kowacce
kabila ‘yancinta, kar a ce an danne wani yanki a jihar. H za ta dauki
SHAWARORI TAKWAS GA MASU CIKI SHAWARORI ZUWA GA MASU CIKI
*********************************
Wayannan shawarori zasu amfani mata masu ciki sosai da sosai ta 'bangaren lafiyarki da jaririnki tare kuma da fatan samun na tsatstsen yaro.
1. Yana da kyau Macce me ciki ta siffantu da halaye na kwarai tare kuma da gujewa munanen halaye.
2. Saurarar karatun Alqur'ani na mintuna 30 kullum ga macce mai ciki kan taimaka wajen samun natsatstsen yaro.
3. Kauracewa duk wani magani da ba likita ne ya bada umurnin a sha ba, kan taimaka wajen samun lafiyayen jariri.
4. Macce mai ciki ta guji rashin yin bacci da wuri, samun bacci na awa 8 kan taimaka wa kwakwalwar jaririn da za'a haifa.
5. Macce mai ciki ta guji aikin wahala ko kuma wani abu wanda yayi kama da shi domin samun lafiyar jikinta da ta jariri.
6. Mai ciki ta rika kula da abinci kafin taci, ta tabbatar baku tsakuwa ko datti a cikin abinda zata sha.
7. Yawaita cin kayan lambu irinsu, Zogale, Cucumber, kankana, lettuce, alayyahu da sauransu.
8. A karshe yana da kyau mai ciki ta rika cin dabino hudu a rana biyu da safe biyu da dare koma fiye da su.
Allah ya baku ikon saukewa, masu nema Allah ya basu, wayanda ke da Allah ya basu abin ciyarwa da ikon tarbiyantarwa.
Subscribe to:
Posts (Atom)